✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwadago ba su hallara a zaman da Buhari ya kira ba

An dage taron zuwa ranar Talata saboda kungiyoyi kwadago ba su hallara ba

Kungiyoyin kwadago sun gaza halartar taron tattaunawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kira kan karin kudin wutar lantarki da na man fetur.

A ranar Juma’a Buhari ya umarci Ministan Kwadago, Chris Ngige ya zauna da kungiyoyin kan batun ranar Asabar, amma ba su hallara ba, lamarin da ya sa aka dage taron zuwa ranar Talata, 15 ga Satumba, 2020.

Mataimakin Darektan Watsa Labarai na Ma’aikatar Kwadago, Charles Akpan ya ce dagewar ta zama dole saboda bisa alamu kungiyoyin ba za su iya hallara gaba daya ranar Asabar ba.

Majiyarmu ta ce Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi korafin cewa gayyatar ta zo a kurarren lokacin da ba za ta iya hado kungiyoyin karkashinta ba su samu halarta.

A wani kaulin kuma, Kungiyar Gamayyar Ma’aikata (TUC) ta shirya halartar taron na ranar Asabar.

Tun da farko TUC ta ba Gwamnati zuwa ranar Litinin ta janye karin farashin mai da na wutar lantarki ko kuma ma’aikata su shiga yajin aiki.

Yanzu da umarnin adage zaman tattaunawar, da alama TUC ta kara wa’adin da ta ba wa gwamantin ke nan.