✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin ’yan makaranta sun bijire wa matakan kariya a Jihar Kano?

Gaskiya na ji dadin dawowa makaranta domin wannan zai ba mu dama mu karasa karatunmu

A ranar Litinin, 18 ga watan Janairun 2021, Gwamnatin Jihar Kano ta sake bude makarantu bayan rufewar da ta yi a watan Disamba da nufin dakile annobar cutar Coronavirus a zagaye na biyu.

A zagayen da Aminiya ta yi a wasu daga cikin makarantun da ke jihar da suka hada da na firamare da sakandire da kuma manyan makarantu ta iske cewa dalibai da dama sun dawo da shaukin son komawa makarantar.

Sai dai Aminiya ta gano cewa akwai karancin bin dokokin matakan kariya daga daliban duba da cewa yawancinsu ba su sanya takunkumin rufe fuska ba ballantana kuma bayar da tazara tsakaninsu.

Sai dai a makarantun da Aminiya ta zagaya ta iske cewa hukumomin makarantun sun samar da kayayyakin kariya daga annobar ta Coronavirus irin su sabulun wankin hannu da na gogewa wanda aka ajiye a wurare daban daban a cikin makarantun.

Ziyarar Aminiya a Kwalejin Sa’adatu Rimi ya iske dalibai sun dawo makarantar tare da burin son yin karatu.

Wata daliba Zulaihat Shehu ta bayyana ceewa “Na ji dadi da aka dawo makaranta yau domin ina fatan mu samu mu ci gaba da karatunmu kasancewar a wancan lokaci muna gab da fara jarrabawa aka rufe makarantar.”

Daliba Zulaiha ta nuna damuwarta game da yadda ba a fara karatu a makarantar ba inda ta ce, “Tunda muka zo muke jira mu ga ko malamai za su shiga aji amma har yanzu babu malamin da ya shiga ajinmu.

“Muna fatan dai malaman su mayar da hankali ko ma samu mu karasa karatunmu kada azo asake rufe makarantun,” in ji Zulaiha.

Ita ma daliba Rukayya Adam Idris ta bayyana cewa, “Gaskiya na ji dadin dawowa makaranta a yau, domin wannan zai ba mu dama mu karasa karatunmu kamar yadda muka faro kan lokaci.

Dalibar ta yi kira ga gwamnatin da ta taimaka musu a kan kada ta sake rufe makaranta a nan gaba.

“Muna kira da gwamnati da kada ta sake rufe makarantu a nan gaba, za mu yi kokarin bin dukkanin matakan kariyar da aka sanya wajen gujewa yada annobar Coroavirus.

“Idan ma da wasu tsare-tsare da gwamnatin za ta fito da shi to mu za mu bi a maimakon rufe mana makaranta, domin a baya mun sha wuya har muka gaji da zaman gida.”

Sai dai abin ba haka yake a makarantu masu zaman kansu ba domin Aminiya ta gano cewa yawancin makarantun sun ci gaba da gudanar da darussa a ajujuwansu.

Aminiya ta ziyarci Makarantar Salam International School Fagge malamai sun shiga aji inda suka ci gaba da gudanar da darusaa kamar yadda aka saba.

Dalibi Ahmad Lawan ya shaidawa Aminiya cewa “Alhamdulillahi yau mun komo makaranta an canza mana aji kafin a yi hutu ina aji hudu yanzu kuma na shiga aji biyar na sakandire har ma an yi mana karatun inda malamin Physics ya shiga ajinmu.”

Kazalika, Aminiya ta kai ziyara Makarantar Sakandiren Maza ta Magwan inda ta iske an tanadi kayyayakin kariya na dakile yaduwar cutar COVID-19.

Haka kuma an sami dalibai suna  ajujuwa wadanda suka kasance cikin shirin ci gaba da daukar darussa.

Haka halin yake a Makarantar Firamare ta Kano Capital inda Aminiya ta iske dalibai sun dawo makaranta cikin yanayin kariya na dakile yaduwar annobar.

Abubakar Abdullahi dalibi ne a makarantar ya bayyana cewa ya yi murna da aka dawo makaranta ya kuma bayyana cewa yana bin matakan kariya.

A cewarsa, “Na ji dadi da aka dawowa makaranta kuma zan bi matakan kariya domin iyayena sun nuna min cewa dole na rika sanya takunkumi a fuskata kuma sun gaya min na rika nisanta kaina daga jama’a.”