✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan taratsi sun umarci kamfanonin mai su fice daga Akwa Ibom

Suna zargin kamfanonin da aikata barna al’ummomi masu arzikin mai.

Wasu ’yan taratsi sun ba wa kamfanonin hakar mai umarnin ficewa daga Jihar Akwa Ibom nan take.

Kungiyar ’yan taratsin karkashin inuwar Unyekisong Akwa Ibom ta ce ta ba da umarnin ne saboda abin da suka kira barnar da kamfanonin suke yi a al’ummomi masu arzikin mai.

Sanarwar da Shugabannin kungiyar, Dede Udofia da Ibanga Ekang, suka fitar ta ce ya zama wajibi kamfanonin sun fice daga yankin tunda ba sa amfanar al’ummomin da suke hakar mai da komin.

Sanarwar ta ce in banda kamfanonin hakar mai na ExxonMobil Savannah, duk sauran kamfanonin sun ki yin ayyukan taimakon al’ummomin yankin da suke amfana da arzikin mansu.