✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanzu ana damawa da mata a jihar Kaduna – Balaraba Salisu

Wata fitacciyar ‘yar siyasa mai fafutikar ganin mata sun shigo an dama da su a siyasar Jihar Kaduna da kasa baki xaya, Hajiya Balaraba Salisu…

Wata fitacciyar ‘yar siyasa mai fafutikar ganin mata sun shigo an dama da su a siyasar Jihar Kaduna da kasa baki xaya, Hajiya Balaraba Salisu Bala ta yaba da yadda Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-rufai ke damawa da mata a cikin gwamnatinsa.

Hajiya Balaraba wadda ita ce shugaban riko na matan jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, ta yi wannan jawabin ne a lokacin da take zantawa da wakilin Aminiya a Kaduna, inda ta ce Gwamnan Kaduna ya ciri tuta a cikin sauran gwamnoni, domin kuwa shi ba ya nuna wariya ko son kai a tsakanin mata da maza a siyasar jihar.

A cewarta, a da can, Jihar Kaduna na xaya daga cikin jihohin da ba a damawa da mata a harkar siyasa, duk kuwa da cewa matan suna taka rawar gani sosai a duk lokacin da aka buga gangar siyasa, sannan kuma matan ne kusan kashi 50 na mutanen jihar, kuma babu wanda zai samu nasarar lashe zabe ba tare da taimakon matan jihar ba, amma Gwamna El-rufai ya canza wannan tsarin. 

“Dole ne mu yaba wa Gwamna Nasiru Elrufai domin shi mutum ne mai adalci da sanin ya kamata. A da can an mayar da mu saniyar ware a harkar siyasar Jihar Kaduna. Ba a nemanmu sai lokacin siyasa kawai. Idan an samu nasara sai a yi watsi da mu sai kuma idan siyasa ta zagayo. Amma da yake adalin shugaba ne mai sanin ya kamata, sai ya janyo mata cikin lamarin siyasar, domin a dama da mu, wanda kuma ba a saba mana da hakan ba,” inji Balaraba Salisu Bala.

Da ta juya kan batun mulki kuwa, Hajiya Balaraba Salisu Bala ta tabbatar da cewa duk xan Jihar Kaduna da ma mazauna jihar, ya san cewa Gwamna El-rufai mutum ne mai faxa da cikawa. Domin kuwa duk lungu da sakon jihar, babu inda aikin gwamna El-rufai bai kai ba.

“Gwamna Elrufai ya cika duk alkawuran da ya xauka. Ya samar wa dubban mutane aikin yi a kowane bangare. Ga ayyuka nan a kowane lungu da sakon jihar, abin dai ba a cewa komai sai kawai godiya da sa albarka.

“Ni a matsayina na mai wakiltar mata, muna godiya, kuma muna cewa Allah Ya maimaita mana,” inji Balaraba.

A karshe sai hajiya Balaraba ta yi kira ga xaukacin ‘yan siyasar Kaduna da su haxa hannu da Gwamna Elrufai wajen ciyar da jihar gaba.

“Ina kira ga ‘yan siyasar Kaduna da mu haxa hannu da Gwamna  Elrufai domin ciyar da jihar gaba. Domin babu komai a zuciyarsa sai alheri. 

“Sannan ina kara kira ga mata ‘yan uwana da su shigo a dama da su a cikin harkar siyasa, domin nan gaba muna sa ran mu karba ragamar mulkin” inji ta.