✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yarabawa ba su da shugabanni -Edwin Clark

Muna da shugabbani – Afenifere Wani tsohon Ministan Watsa Labarai kuma jagoran kabilar Ijaw, Cif Edwin Clark ya ce Yarbawa ba su da shugaba, inda…

Muna da shugabbani – Afenifere

Cif Edwin ClarkWani tsohon Ministan Watsa Labarai kuma jagoran kabilar Ijaw, Cif Edwin Clark ya ce Yarbawa ba su da shugaba, inda ya ce Tinubu da sauransu da suke nuna shugabanninsu za a iya saye cikin sauki.
Ya bayyana haka ne a shekaranjya Laraba a gidansa a Abuja, lokacin da shugabannin al’ummun Kudu maso Kudu da ke Abuja suka kai masa ziyarar girmamawa.
Ya ce tun mutuwar marigayi Cif Adekunle Ajasin da Pa Abraham Adesanya da Cif Bola Ige, babu wani shugaban Yarbawa da ya bayyana.
A cewarsa, “Asuwaju Bola Ahmed Tinubu da sauransu mutane ne da kudi zai iya sayensu, amma kudi ba zai sayi shuagabanci ba. Suna tunanin Shugaba Jonathan ba zai iya kiran taron kasa ba.”
Ya ce, “Har yanzu ina da imani kan hadin kan Najeriya, shekara 100 ta wuce wannan ya sa muke cewa mu samu taron kasa don tattauna yadda za mu zauna tare nan da wasu shekara 100 masu zuwa.”
 Sai dai a martanin Kakakin Afeniferi, Yinka Odumakin ya ce Yarbawa suna shugabanni, amma ba su da shugaba guda daya a yanzu.
“Yarbawa suna da shugabanni ko jagorori, amma ba su da jagora guda daya a yanzu. Kuma wani ya ce ana ya sayen wasu mutane, kodai wadancan mutane an taba sayensu a baya ko sun sanya farashi,” inji Odumakin.