✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yarinya Ese: Fiye da lauyoyi 20 za su kare Yunusa – Barista Bukarti

An tafka maharawa mai zafi yayin da aka ci gaba da sauraron shari’ar matashin nan Yunusa dahiru da aka fi sani da Yellow wanda ake…

An tafka maharawa mai zafi yayin da aka ci gaba da sauraron shari’ar matashin nan Yunusa dahiru da aka fi sani da Yellow wanda ake zargi da sace budurwarsa Ese Oruru tare da musuluntar da ita don ya aure ta a ranar litinin da ta gabata a Yenagoa, fadar Jihar Bayelsa.
Lauya mai gabatar da kara Kenneth Dika, ya nemi alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Yenagoa inda ake shari’ar, Mai shari’a H. A. Nganjiwa ya saurari jawaban Ese a asirce domin a cewarsa yarinya ce wadda a ka’idar tsarin mulki ba ta cancanci gurfana a gaban kotu ba.  
Sai dai lauyan wanda ake kara Kayode Olaoshebikan ya ki amincewa da bukatar haka.
Kotun dai tana tuhumar dahiru da laifin dauke yarinyar ya boye ta daga wurin iyayenta tare da saninta, wanda hakan ya saba wa doka, laifin da saurayin ya ki amincewa ya aikata.
Lauyan dahiru ya nemi kotu ta duba maganar bayar da belinsa da aka nema a ranar Litinin din makon jiya, amma sai alkalin ya sake dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar Litinin mai zuwa 21 ga watan Maris.
Wani rukunin lauyoyi da suka dauki nauyin kare Yunusa dahiru a shari’a da suka hada da Barista Audu Bulama Bukarti da Barista Huwaila Muhamamd Ibrahim da Barista Khaleefa Sheriff da Barista Olaosebikan Kayode da kuma Barista Aled Oche, sun sha alwashin ganin an yi wa saurayin adalci.
Aminiya ta tattauna da Barista Abdu Bulama Bukarti ta tarho game da yadda zaman kotun ya gudana inda ya ce lauyoyin da suke kare Yunusa sun nuna rashin amincewa kan bukatar da masu gabatar da kara suka yi suna nemam kotu ta gudanar da shari’ar cikin sirri, saboda dalili na karancin shekaru Ese.
“Mun ce ba mu yarda da bukatarsu ta kin gabatar da Ese a gaban kotu ba, domin hakan zai iya kawo rashin adalci a shari’ar gaba daya. Mun ce idan suna maganar kare hakkin yarinya to ai tuni kowa ya san muryarta da fuskarta saboda yadda labarin ya watsu a kafafen watsa labarai na ciki da wajen kasar nan. Don haka batun kin bayyanarta a kotu bai taso ba,” inji shi.
Game da batun belin Yunusa, Barista Bukarti wanda malami ne a Tsangayar Koyar da Aikin Lauya ta Jami’ar Bayero da ke Kano ya ce sun yi duk yadda za su yi a kan a ba su belin yaron amma hakan bai samu ba, har alkalin kotun Mai shari’a H.A. Nganjiwa ya dage shari’ar zuwa ranar 21 ga Maris inda ake sa ran zai yanke hukunci a kan batun belin Yunusa da gudanar da shari’ar cikin sirri.
Barista Bukarti ya ce sun nemi jami’an gidan kurkukun da ke tsare da Yunusa da su sanya ido kan yadda ake cin zarfinsa a kurkukun. Domin ya yi korafin cewa wasu ma’aikatan kurkukun da masu zaman wakafi da suke da bambancin addini da kabila da shi suna cin zarafinsa.
Bukarti ya ce Yunusa ya bayyana musu cewa da farko da aka kai shi jami’an kurkukun sun doddoke shi. Sai kuma bayanin da ya yi cewa abokan zamansa na kurkuku suna dukansa da zaginsa cewa ya dauke musu ’yar uwa ya musuluntar da ita. “Hakan ya sa muka yi magana da jami’an kurkukun a kan su dauki mataki ko kuma mu dauki matakin shari’a a kai. Sun nuna mana cewa ba su san abin da ke faruwa ba, tare da yin alkawarin hakan ba za ta ci gaba da faruwa ba. Mun so mu ba shi kudi ya ki karba inda ya ce idan ya tafi da kudin kwacewa za su yi. Sai muka ba jami’an gidan yarin kudin tare da umartar wani lauya daga cikinmu mazaunin Bayelsa ya rika bibiyar lamarin Yunusa da yadda ake ba shi kudin da kula da halin da yake ciki a kurkukun gaba daya,” inji Bukarti.
Barista Bukarti ya ce duk da cewa ba su samu belin Yunusa ba, halartarsu kotun na ranar Litinin da ta gabata kawai wata gaba ce da ke nuna nasara gare su. Ya ce yanzu haka akwai lauyoyi sama da 20 da suka nuna sha’awarsu ta kare wannan yaro. Baya ga lauyoyi daga Kano da Kaduna da Abuja, a can Bayelsa ma sun dauki wasu lauyoyin biyu da za su taimaka musu.
Ya ce suna sa ran samun nasara idan har aka yi la’akari da yadda shari’ar take tun fark domin ko su masu gabatar da kara sun bayyana wa kotu cewa yarinyar da yaron tafiya suka yi tare ba sace ta ya yi ba.