✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben kananan hukumomin Jihar Kebbi ya bar baya da kura

A ranar Asabar da ta gabata ce aka gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar Kebbi, inda aka ce an gudanar da zaben a dukkan…

A ranar Asabar da ta gabata ce aka gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar Kebbi, inda aka ce an gudanar da zaben a dukkan kananan hukumomin jihar.

Sai dai a zantawar da wakilinmu ya yi da Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kebbi Alhaji Haruna D. Sa’idu, ya ce ba a yi zabe a jihar ba.

Ya ce Jam’iyyar APC ta yiwo hayar ’yan bangar siyasa ne kawai suka rika tare hanyoyi suna kwace kayan zabe suna shiga gidajen manyan ’ya’yan Jam’iyyar APC suna dangwala kuri’u.

Ya ce akwai wani Sarki da ya ce ya fito kofar gidansa domin ya jefa kuri’a amma har zuwa yamma ba a kawo akwatin kofar gidansa ba, kuma ya ce yawancin gidajen da aka shiga aka dangwala kuri’un suna da faifan bidiyon haka. Shugaban ya ce a Karamar Hukumar Argungu, Babban Jami’in zabe mai fadar sakamako wanda malamin jami’a ne karfe 12:00 na rana ya fadi sakamako.

“Saboda haka zabe a Jihar Kebbi ba a yi  ba, Jam’iyyar APC da Gwamnatin Jihar Kebbi sun yi yadda suka ga dama amma za mu kalubalance su,” inji shi.

Sai dai a martanin da ya yi a kan zarge-zargen Shugaban Jam’iyyar PDP kan zaben kananan hukumomin da aka gudanar, Shugaban Jam’iyyar APC Alhaji Bala Sani Kangiwa,  ya ce wadannan zarge-zarge magana ce wacce ba ta da tushe balle makama. “Kuma da ya ce ’ya’yan APC sun tare hanya sun kwace kayan zabe a Karamar Hukumar Argungu ba gaskiya ba ce, saboda da APC ta yi rashin gaskiya a Karamar Hukumar Argungu PDP ba za ta samu cin kansila ba,” inji shi.

Ya ci gaba da cewar Jam’iyyar PDP ta saba da handama da babakere shi ya sa take zargin Jam’iyyar APC da hakan.