✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamba: ‘Yan sanda sun maka ma’aikacin NIPOST a kotu

Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wani ma’aikacin Hukumar rarraba wasiku NIPOST a gaban kotu bisa zargin amfani da takardar jabu don yin zamba. Wanda…

Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wani ma’aikacin Hukumar rarraba wasiku NIPOST a gaban kotu bisa zargin amfani da takardar jabu don yin zamba.

Wanda ake zargin mai suna Daniel Ishaku, an gurfanar da shi ne a gaban kotun majistari da ke a unguwar Wuse 2 a birnin tarayya Abuja.

Ana zargin wanda ake karan ne bisa zambartar wata kungiyar mai suna (Arcuma Multipurpose Cooperative Society Limited) kudi Naira miliyan daya da rabi ta hanyar gabatar da takardun jabu na ma’aikatan NIPOST din.

Mai shigar da kara Peter Ejike, ya fadawa kotun cewa wanda ake karan ya yi amfani da hotuna da sa hannu na wasu ma’aikatan hukumar ta NIPOST a shirin matakin karban bashi.

Peter Ejike ya kara da cewa, wanda ake karar tuni ya amsa laifinsa a lokacin da ‘yan sanda suke gudanar da bincike, inda ya ce sun gano kuma su ne suka karbi kudade kimanin Naira dubu 150 daga wurinsa.

Ya bukaci kotun da ta tuhumi wanda ake karan bisa laifin damfara, zamba da kuma amfani da takardun  jabu wanda ya sabawa sashe na 79, 176 da 364 da kundin dokokin kasa.

Wanda ake karan ya yi watsi da laifufukan da ake zarginsa da shi.

Lauyan wanda ake karar, Barista Obumneme Agbo ya nemi kotun da ta bada belin wanda ake karar, inda ya tabbatarwa kotun cewa wanda ake karan ba zai sabawa ka’idojin belin ba.

Alkalin kotun, Ahmed B. Ndajiwo ya bada belinsa akan Naira miliyan 1 ga wanda ake karan da kuma gabatarda mutum biyu tsayayyu da zasu tsaya masa.

Ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Afrilu shekara ta 2020.