✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zanga

Wani ustazu ne ya jagoranci zanga-zanga, magoya bayansa suna ta hargowa cikin kaimi. Can ba su yi aune ba sai suka ci karo da jami’an…

Wani ustazu ne ya jagoranci zanga-zanga, magoya bayansa suna ta hargowa cikin kaimi. Can ba su yi aune ba sai suka ci karo da jami’an tsaro kowa da bindiga. Sai jagorar zanga-zanga ya ci birki, ya fara nade kafar wando. Sai sauran masu binsa suka ce: “Ustaz, inji dai ba gudu za ka yi ba?” Cikin kakkausar murya ya ce: “Insha Allah!”
Daga Hussaini Muhammad Binanchi da Isa Kwafsi 08087436699