✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zuba jari yau don bunkasa harkar noman gobe

Noma ne babban jigon tattalin arzikin Najeriya, kuma bangare ne da ya fi kowanne wajen samar wa ‘yan kasar aikin yi, kamar yadda alkaluman Bankin…

Noma ne babban jigon tattalin arzikin Najeriya, kuma bangare ne da ya fi kowanne wajen samar wa ‘yan kasar aikin yi, kamar yadda alkaluman Bankin Duniya da na Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) a kan ma’aunin walwalar jama’a suka nuna.

Bangaren na samar wa akalla kashi 60 cikin 100 na al’ummar kasar ayyukan yi musamman a daidaikunsu.

Ana sa ran nan da shekara ta 2050, yawan al’ummar Najeriya zai iya kaiwa kusan miliyan 402, kusan ninki biyu ke nan na yawan mutanen da kasar ke da su a yanzu haka a hasashen Sashen Kula da Tattalin Arziki da Walwalar Jama’a na Majalisar Dinkin Duniya.

Karuwar jama’ar zai rubanya bukatar kayayyaki, wanda hakan kuma zai tilasta neman kari a kan yawan kayan abincin da za a bukata a nan gaba.

Bankin Sterling ya tattara masu ruwa da tsaki don neman mafita

Saboda damuwa game da yiwuwar fuskantar karancin abinci a Najeriya, bankin kasuwanci na Sterling ya tattara masana da masu ruwa da tsaki don tattaunawa ta inatnet a kan yadda za a bunkasa harkar noman ta hanyar zuba jari da fasaha da kirkire-kirkire.

Tattaunawar mai taken “Zuba jari a yau don bunkasa harkar noma gobe”, ta tattaro kwararru daga gida da kasashen ketare kan harkar noma don riba kuma babban darakta mai kula da bangaren zuba jari na bankin, Mista Yemi Odubiyi, ya jagorance shi.

Annobar corona ta zo da darasi

Da yake jawabin bude taron, Mista Odubiyi ya ce annobar coronavirus ta nuna karara cewa ba zai yiwu ba Najeriya ta ci gaba da dogaro da abincin da aka shigo da shi daga ketare.

Ya lura cewa Najeriya na da damar da za ta bunkasa tattalin arzikinta ta hanyar bunkasa harkar noma, yana mai cewa harkar ce ta fi samar wa mutane ayyukan yi a kasar.

Babban daraktan ya kuma ce tun shekaru hudu da suka shude, bankin na Sterling ya ware kashi 10 cikin 100 na basussukan da ya ke rabawa domin bunkasa harkar.

Ya ce sannu a hankali bankin ya mayar da hankalinsa kan bunkasa harkokin lafiya, ilimi, noma, samar da makamashin da ba ya gurbata muhalli da kuma harkar sufuri.

Bankin zai tallafawa manoma

Bukola Awosanya, shugabar sashen noma da ma’adinai na bankin ta ce tuni suka dukufa wajen samar da kudade da shawarwari don tabbatar da cewa harkar na kawo riba yadda ya kamata.

Awosanya wadda kuma ita ce shugabar wata kungiya mai rajin samar wa mazauna karkara a nahiyar Afirka basussuka don bunkasa harkokinsu na noma mai suna (AFRACA) ta ce fasahar zamani na da matukar muhimmanci wajen bunkasa harkar noma musamman a wannan zamanin, tana mai jaddada cewa hakan ne ma ya sa bankin nasu ya dukufa wajen tallafa wa harkar.

“Mu a bankin Sterling mu kan tsara tare da kirkiro hanyoyin fasahar zamani don mu bunkasa harkar noma”, inji ta.

Da ya ke nasa jawabin, manajan daraktan kungiyar bunkasa noma ta Africa Green Revolution Forum (AGRF), wadda daya ce daga cikin manyan kungiyoyin duniya masu fafutukar habaka noma a nahiyar Afirka, Adebisi Araba, ya ce, “Muna fama da annoba da ta addabi duniya wadda ke barazana ga duk wasu tsare-tsare na tattalin arziki da walwala.

“Mun fahimci bukatar rage tazarar da ke tsakanin masu shi da mara sa shi tare da takaita rashin daidaiton da ke tsakaninsu”.

‘Rancen da bankuna ke ba manoma ya yi kadan’

Mista Araba ya kuma lura cewa kashi hudu cikin 100 ne kacal na basussukan da bankuna ke bayarwa ya ke tafiya wajen harkar noma, harkar man fetur da iskar gas kuma na samun kashi 27 cikin 100, gwamnatin tarayya kashi 9 cikin 100, yayin da harkar ilimi ba ta samun ko da kashi daya.

Ya lura cewa wannan babban kalubale ne ga harkar noma musamman a yunkurin da kasar ke yi na farfado da tattalin arzikinta musamman ta bangaren kamfanoni masu zaman kan su.

Araba ya kuma yi hasashen cewa akwai alamun haske a harkar noman daga nan zuwa shekara ta 2030, musamman idan aka yi la’akari da irin kudaden da ake narkawa wajen zuba jari a harkar da kuma irin sabbin fasahohin da ake kirkirowa a kullum.

“Akwai kyakkyawan fatan cewa nan ba da jimawa ba Najeriya za ta rage yawan dogaron da take a kan shigo da kayan abinci daga kasashen da ta fi su damar da kuma albarkatun noman”, inji shi.

‘Bukatar kayan abinci za ta ci gaba da karuwa’

Da ya ke bayar da tasa gudunmawar, shugaban kamfanin Musoni Kenya Limited,  Mista Stanley Munyao, ya ce bukatar kayan abinci za ta ci gaba da karuwa yayin da yawan jama’a ma ya ke karuwa a kullum.

A kan haka ya bayyana cewa ya zama wajibi kasar ta taimaka wa kananan manoma da tallafi don ganin sun bunkasa harkokin nasu daga na gargajiya zuwa na zamani.

A cewarsa, babbar hanyar da za a bi don cimma wannan burin ita ce samar wa manoman basussuka masu saukin biya da kuma samar musu wayoyin hannu don su samu zarafin tattaunawa da malaman gona kai tsaye idan bukatar hakan ta taso.

Shi kuwa babban manajan kamfanin da ke samar da kudaden tallafa wa harkar noma na Sahel Capital, Mezou Nwuneli ya ce akwai bukatar ganin an samar da isassun kudade ga manya da kananan manoma.

Ya ba da shawarar zakulo kamfanonin da a baya suka taka rawar gani a bangaren don karfafa musu gwiwa, yana mai cewa ta hakan ne za a janyo hankalin hukumomin kudi na duniya domin su ma su shigo su bayar da tasu gudunmawar musamman ta fuskar zuba jari.

‘Manoma na bukatar karin tallafi daga bankuna’

Shi kuwa a nasa bangaren, manajan kamfanin samar da takin zamani na OCP a Najeriya, Mista Caleb Oseh, ya ce akwai bukatar bankuna da sauran hukumomin kudi su kara hobbasa wajen zakulowa tare da tallafawa kananan manoma, musamman wadanda ba su da manyan kadarorin da za su iya bayarwa jingina, saboda ya ce su ne kashin bayan samar da abincin a kasashen Afirka.

Shugaban kamfanin AFEX Commodities Exchange, Ayodeji Balogun ne dai ya jagoranci tattaunawar in da a tasa gudunmawar ya bukaci bankin na Sterling da ya shige gaba wajen tattauna makomar harkar noman.

Ya lura cewa, “A baya mun dade muna magana kan yadda hakan mu zai cimma ruwa wajen bunkasa harkar noma ba tare da tattauna yadda za mu samar da kudaden yin hakan ba. Wannan shine karon farko da aka yi hobbasa wajen tabbatar da hakan”.