✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tagwayen da suka ziyarci kasashe 53 kafin su cika shekara a duniya

Sun tafiyar kimanin mil 31,000 a sararin samaniya a cikin jirgi.

Na zaune bai ga gari ba,” in ji masu iya magana, amma babu wanda ya yi amanna da wannan karin magana da kuma kokarin aiki da shi irin wata ma’aikaciyar jinya ’yar kasar Ingila mai suna Karen Edwards da mijinta Shaun Bayes wadanda suka dauki ’ya’yansu tagwaye zuwa sassan duniya, suka kuma kewaya da su kasashe 53 a nahiyoyi 5.

Sun kuma ci kimanin mil 31,000 a sararin samaniya a cikin jirgi.

Karen Edwards ta haifi ’yan tagwaye Fionn da Fern ne a watan Janairun bara a Asibitin Dannat El Emerat da ke babban birnin Hadddiyar Daular Larabawa.

Kuma ta yanke shawarar tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya da tagwayen, domin su ga garuruwa da kasashe su bude ido.

Karen ta yi amfani da hutunta na haihuwa na wata uku domin wannan tafiya a karon farko, inda ta fara zuwa wa da su kasar Switziland da Oman inda suka kwashe wata biyu.

Sai kuma ta yi amfani da sauran wata gudan da ya rage ta je Ingila don nuna wa ’yan uwa da dangi da abokai abin da ta haifa na ’yan kwanaki, kafin ta lula zuwa kasar Sri Lanka da su.

Da alama yawon duniya a jikin Karen da mijinta Shaun yake, domin a lokacin da suka haifi ’yarsu ta fari mai suna Esmi mai shekara takwas a yanzu, sai da ita ma suka karade kasashe 53 a nahiyoyi shida da ita.

Haka ma da ta haifi kaninta mai suna Kuinn sai da suka karade kasashe 40 a nahiyoyi shida da shi.

Karen ba ta huta da yawo a jirgin sama tana ziyartar kasashe ba sai a lokacin annobar Kwarona wadda ta rutsa da su a Ingila, kuma hakan ya tilasta musu zaman gida na tsawon lokacin da aka sa dokar kulle a kasashen duniya gudun yada cutar.

Ana cikin haka, dama ta samu ga Karen, inda ta samu aikin jinya a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a wani asibiti mai zaman kansa, kuma aka ba ta mukamin shugaba, da albashi da alawus mai tsoka, hakan ya sa ta sake dibar ’ya’yan nata da tagwaye zuwa yawon bude ido.

Fa’idar tafiye-tafiyen da ta yi

A cewar Karen, wadannan tafiye-tafiye da ta yi da tagwayenta da kuma yayyensu sun yi musu rana, domin sun karu da wasu abubuwa na zaman duniya da rayuwa a kasashen da suka ziyarta, “Sun yi abokai Musulmi da yawa.

“Yanzu kuma sun koyi zamantakewa a kasar mabiya addinin Buddha,” in ji Karen. Sannan ta ce, “Sun ga namun daji da yawa da idanunsu, ba a littafi ba.

Haka sun je Tekun Rum da Tekun Fasha da kuma babban kogin da ya ratsa Ingila da Faransa sun kuma yi tafiya a cikin kwale-kwale.” Lallai na zaune bai ga gari ba.

Dangane da ilimi kuwa, Karen ta ce, “Daga koyon harshen Larabci zuwa kafa tanti a gabar teku da suka koya ta tabbata hakan zai yi musu amfani nan gaba a rayuwa, idan sun girma.”