✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taho-mu-gamar jirgin kasa ta kashe mutum 40 a Pakistan

Fasinjoji sun makale a cikin jiragen kasan da suka yi karo a safiyar Litinin.

Akalla mutum 40 ne suka mutu wasu fiye da 120 kuma suka jikkata a wata taho-mu-gamar jiragen kasa a kasar Pakistan.

Wani bidiyon wajen da hadarin ya auku ya nuna tarkacen jiragen kasan biyu da suka yi taho-mu-gamar makale a layin dogo, inda masu aikin ceto ke amfani da injina domin kaiwa ga mutanen da suka makale.

Babban jami’in ’yan sandan garin Dharki, Umar Tufail, ya ce, “Kan jirgin kasan ya danne daya daga cikin taragan, sannan muna iya hango gawarwaki uku da suka makale a ciki.

“An kuma samu rahoton ganin wasu gawarwaki biyu a wani wajen na daban, don haka muna fargabar yiwuwar kara samun mace-macen zuwa lokacin da za kammala aikin ceton,” kamar yadda ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na AFP.

Babban jami’in ’yan sandan ya kuma tabbatar da rasuwar mutum 40, a hatsarin da ya faru da sanyin safiyar Litinin a kusa da garin Dharki, mai nisan kilomita 440 a Arewa da Karachi, birni mafi girma a Pakistan.