✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taho-mu-gamar ’yan dabar siyasa ta yi sanadiyyar rasa rai a Jigawa

Babura ce dai asalin Karamar Hukumar da Gwamna Badaru Abubakar ya fito.

Akalla mutum daya rasa ransa, wasu biyu kuma sun jikkata bayan wasu ’yan dabar siyasa da ba sa ga maciji da juna sun yi taho-mu-gama a Karamar Hukumar Babura ta jihar Jigawa.

Babura ce dai asalin Karamar Hukumar da Gwamnan Jihar Mohammed Badaru Abubakar ya fito.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi, yayin bikin kaddamar da aikin hanyar cikin gari a Karamar Hukumar, wacce Gwamnatin Jihar za ta fara ginawa

Sai dai kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, ASP Zubairu Aminuddeen ya ce babu wanda ya rasa ransa a rikicin, amma sun sami rahoton jikkata.

Ya ce wadanda suka sami raunukan sun hada da wani mai suna Sadisu Mohammed da Abubakar Mahmud da ma wasu.

ASP Zubairu ya kuma ce tuni zaman lafiya ya dawo yankin bayan sun kwantar da tarzomar.

Rahotanni sun nuna cewa taho-mu-gamar ta samo asali ne kan kokarin gwada kwanji kan wanda zai karbi ragamar jam’iyyar APC mai mulki a jihar gabanin zaben 2023.

An dai yi ittifakin cewa lamarin ya kara rura wutar zaman doya da manja da aka jima ana yi tsakanin Kananan Hukumomin Gumel da Babura.