Daily Trust Aminiya - Takaitaccen tarihin Sarakunan Fulani na Kano (2)
Subscribe

Sarki Muhammadu Sanusi I

Takaitaccen tarihin Sarakunan Fulani na Kano (2)

A makon jiya muka shiga taskar rumbun ilimi inda muka fara kawo takaitaccen tarihin sarakunan Fulani wadanda suka fara mulkin kasar Kano tun daga jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo kawo yau. To yau ga ci gaba kamar haka:

Aliyu dan Abdullahi, 1894 -1903 Miladiyya

Sarki Aliyu ɗan Abdullahi wanda aka fi sani da Sarki Alu. Shi ne Sarki na 50 a jerin Sarakunan Kano, sannan kuma Sarki na 7 a jerin Sarakunan Fulani.

Ya shiga gidan sarautar Kano bayan ya ci Sarki Tukur da yaƙi a garin Tafashiya. Da shigarsa gidan saurata sai ya sa aka riƙa bi gida-gida ana kamo talakawa ana kashewa wadansu kuma ana mayar da su bayi, kamar yadda ya zo a cikin littafin Labarun Hausawa da Maƙwabtansu Littafi na Biyu (1979).

Daga sunayen da ake kiransa da su akwai Alu Mai Sango. Wannan suna ya samo asali ne saboda wasu irin dogayen alburusan bindiga da yake amfani da su wanda tarihi ya nuna cewa Sarkin Nupe ne ya aika masa da su.

A zamanin Sarki Alu, Kano ta yi yaƙe-yake da dama, waɗanda masana ke cewa da kamar wuya, gurguwa da auren nesa, a iya tantance yawan yaƙe-yaken da ya yi. Daga cikin garuruwan da Sarki Alu ya yi munanan yaƙe-yake da su akwai Damagaran.

Tun zamanin Sarkin Kano Bello, wadansu Kanawa suka je Damagaran kasuwanci, sai aka kama su aka yi musu wasoson dukiya. Da Sarki Bello ya tura jakada don jin bahasi, Sarkin Damagaran na wancan lokaci bai ba shi wata cikakkiyar amsa ba.

Tarihi ya nuna cewa, a zamanin Sarki Alu, Sarkin Damagaran ya nufo Kano da yaƙi. Maimakon ya taho Kano kai-tsaye sai ya tura wa Sarkin Sankara cewa yana nan tafe. Da Sarkin Sankara ya samu wannan saƙo, sai ya sanar da wani malami da yake tare da shi. Wannan malami mai suna Malam Almajir, sai ya yi wasu abubuwa irin nasa, ya kewaya garin Sankara, sai ya ce da Sarki ya mayar wa Sarkin Damagaran amsa cewa ƙarya yake bai isa ba. Da wannan amsa ta kai kunnen Sarkin Damagaran, sai ya hau ya nufo Sankara gadan-gadan. Da isowarsa Sankara sai ta ɓace masa da gani ya neme ta ya rasa. Sama-ko-ƙasa.  Shi ke nan, daga nan sai ya zarce zuwa Kano bai tsaya ko’ina ba sai Gezawa, inda a nan Sarkin Kano Alu ya je ya datse shi.

Cikin jaruman Sarkin Damagaran akwai wani jarumi mai suna Mayana, shi ya fara ɗaura ɗamara ya yi wa Sarkin Damagaran alƙawarin zai kawo masa Sarki Alu. Daga nan ya fara ratsa rundunar Kanawa, da ya iso daf da fadawan Sarki suka yi masa ca, sai Sarki ya dakatar da su, ya ce su ƙyale shi ya ƙaraso. Da isowarsa gaban Sarki sai Sarki Alu ya sa takobi ya yi masa sarar kabewa; wato ya raba shi gida biyu ke nan daga sama zuwa ƙasa.

Da labari ya je kunnen Sarkin Damagaran cewa Mayana ya zama gawa, sai hankalin Damagarawa ya tashi; wato sun san abin na yi ne. Daga nan maza suka gauraya aka yi ta fafatawa har zuwa wani lokaci mai tsawo, Kanawa suka fatattaki Damagarawa. An ce saboda tsabar ruɗewa da Damagarawa suka yi, har cikin kara mata ke bi suna kamo jaruman Damagarawa da hannu suna kashewa. A lokacin wannan yaƙi an ce Sarki Alu ya yi ɓad-da-kama ne ya yi shigar Buzaye, ya shiga cikinsu ya yi ta kisa.

Bayan komawar Sarkin Damagaran gida, sai ya fara bincike kan dalilin da ya saka bai ga garin Sankara ba. Sai ya samu labarin cewa ai wani malami ne mai suna Malam Almajir ya yi aiki irin nasa. Da Sarkin Damagaran ya samu wannan labari, sai da ya bi duk hanyoyin da zai bi, ya samu ganawa da Malam Almajir kuma ya roƙe shi kan cewa ya taimaka masa ya ci Kano da yaƙi. Malam Almajir ya amsa wa Sarkin Damagaran amma da sharaɗin ba zai biyo ta Sankara ba. Jin haka shi ma Sarkin Damagaran ya amince.

Da Sarkin Damagaran ya tashi komawa Kano da yaƙi, sai ya bi ta wani gari mai suna Tattarawa wanda a yanzu yake ƙarƙashin Karamar Hukumar Bichi. Shi kuma Sarki Alu ya je Damargu; ita ma dai duk a cikin Karamar Hukumar Bichi take, sai ya datse shi a can suka fafata. Wannan yaƙi bai yi wa Kanawa daɗi ba, saboda Damagarawa sun yi galaba a kansu. Amma dama tun kafin fita wannan yaƙi da labari ya zo gari, malamai sun gaya wa Sarki Alu cewa kada ya fita, fita a wannan rana ba daɗi a bari sai gobe. Amma da Sarki ya yi shawara da hakimansa da sauran waɗanda suka kamata, sai suka ce da shi ai bari sai gobe tsoro ne, a hau kawai a fita. To a wannan yaƙi sai da Damagarwa suka koro Kanawa har dab da ganuwar gari. A wannan hali ba mafita sai Sarki Alu ya je ya samu malamai suka duƙufa cikin addu’a, sannan a lokaci guda ya nemi agajin Turabulusawa mazauna Kano; wato mutanen Turabulus ke nan, garin da a yanzu yake cikin ƙasar Mali, suka ɗauko bindigoginsu suka hau kan ganuwa suka tsare gari. Ana wannan hali sai zazzaɓi ya sauka wa Sarkin Damagaran, saboda haka sai suka juya suka koma. Wannan shi ya kawo ƙarshen wannan yaƙi.

Fafatawar ƙarshe A tsakanin Sarki Alu da DaMagarawa an yi ta Ce a Bakin Tomas da ke cikin Karamar Hukumar Ɗambatta ta yau. A wannan zamani kuma Sarki Ahmadu ne yake sarautar Damagaran. Da suka yiwo hawa suka ɓullo ta Ɗambatta, sai Sarki Alu ya yi maza-maza ya tare su a Tomas. Haƙiƙa wannan yaƙi kowa bai ji da daɗi ba. Amma dai a ƙarshe Kanawa ne suka galabci Damagarawa bayan sun kori Kanawa har gida. An ce sai da Damagarawa suka kori Kanawa suka koma gida suka shiga ta Ƙofar Kansakali. A nan Sarki Alu ya zambace su kamar yadda dama aka sani ana cewa yaƙi ɗan zamba ne. To hakan ta faru. Da Kanawa suka dawo gida sai Sarki Alu ya ce a bar ƙofar garin a buɗe kada a rufe. Su kuma Damagarwa da suka ga ƙofa a buɗe sai suka sanar da Sarki Ahmadu cewa sun ga ƙofa a buɗe saboda haka za su je har gida su kamo Sarki Alu. Ashe shi kuma Sarki Alu ya laɓe daf da ƙofa, ya yi shiga irin ta Buzaye. Saboda haka duk Buzun da ya shigo nan take sai Sarki Alu ya kashe shi. Haka ya yi ta yi musu, har sai da ta kai halin da su Damagarwa suka fahimci cewa duk fa wanda ya shiga ba ya dawowa. Saboda haka sai suka haƙura suka juya.

Sarki Muhammadu Sanusi I
Sarki Muhammadu Sanusi I

Sannan a zamanin Sarki Alu an samu sa-in-sa a tsakanin Ningi da Kano. Amma saboda Sarki Ɗanyaya yana jin tsoron Sarki Alu sai ya zama ba a gwabza yaƙi ba.

Sannan dai a zamanin Sarki Alu ne gaba ta tsananta a tsakanin Kano da Haɗeja. A wannan zamani Sarki Muhammadu ne yake sarautar Haɗeja.

Sarkin Kano Alu shi ya gina garuruwan Fajewa da Ɗando da Magami da Bura da Kwajali da Musa duk a Kudancin Kano a zamaninsa.

Daga ƙarshe, Sarkin Kano Alu ya tafi kai caffa Sakkwato Turawa suka zo suka ci Kano. Wannan labari na shigar Turawa Kano ya iske sarki Alu a lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa Kano shi da jama’arsa da suka haɗa da sarakuna da hakimai da fadawa da lifidai da sauransu. Da labari ya same su, jama’arsa sun ba shi shawarwari kamar haka: “Kodai ka tsaya mu yi faɗa da Turawa, ko kuma ka nemi sulhu da su”. Wadansu kuma suka ce a’a, ya koma Sakkwato wanda kuma hakan ce ta faru. Sarki Alu da wadansu jama’a suka koma Sakkwato. Wadansu kuma ciki har da Wambai Abbas da Waziri Ahmadu da wadansu jama’ar sai suka ci gaba da tafiya Kano.

Da wannan ayari ya iso Kwatarkwashi sai ya yada zango. A wannan zango nasu sai suka haɗu da Turawa. Zatonsu Damagarawa ne saboda haka sai suka far musu da yaƙi. A karon farko sai aka kashe Waziri Ahmadu, da ɗansa da ɗan morinsa. Haka yaƙi ya ƙare. Wambai Abbas da sauran jama’a suka dawo Kano.

A lokacin da Wambai Abbas ke kan hanyarsa ta komawa Kano, sai Turawa suka tura aka tarbe shi. Wambai Abbas da ayarinsa sun isa Kano ranar Juma’a. Sun shiga Kano ta Ƙofar Kansakali. Kafin shigarsu Kano sai da Turawa suka caccaje kayayyakinsu suka ƙwace dukkan makamansu. Sarki Aliyu  Mai Sango, ya rasu bayan ya yi sarautar Kano ta tsawon shekara tara da wata tara.

Muhammadu Abbas, 1903-1919 Miladiyya

Sarki Muhammadu Abbas shi ne Sarki na 51 a jerin Sarakunan Kano, kuma Sarki na 8 a jerin Sarakunan Fulani, har wa yau kuma shi ne Sarki na farko da Turawa suka fara naɗawa.

Sarki Muhammadu Abbas mutum ne jarumi, kuma mai faɗa da cikawa ko kuma ana iya cewa mutum ne kaifi ɗaya. Ya kasance Sarki mai haƙuri da jama’arsa.

Sarki Abbas ya yi mulki tare da Turawa, saboda haka hakimansa suka samu dama ta dalilin haƙurinsa da kawaicinsa suna iya yin magana kai-tsaye da Turawa, har sai da ta kai munafunci ya fara gudana a tsakanin Turawan nan da wadansu daga cikin hakiman Sarki Abbas. Irin wannan lamari na tsaka da faruwa sai Allah Ya kawo wani Bature mai suna Mista Temple, shi ya taka wa wannan al’ada birki. Ya samar da kyakkyawan tsari, ya yanka wa sarakuna da sauran ma’aika albashi. A zamanin Sarki Abbas ne aka yi wani gagarumin taron sarakuna, Gabas da Yamma, Kudu da Arewa a 1912. A zamanin Sarki Abbas ne aka gina wasu kasuwanni a Kano. Sannan a zamaninsa ne a 1910 aka gina wata makaranta a cikin Nasarawa wacce a yanzu ta koma Gidan Ɗanhausa.

Sarki Muhammadu Abbas ya yi sarautar Kano ta tsawon shekara 16. Ya rasu a 1919. An binne shi a gidansa da ke Nassarawa.

Usman dan Abdullahi, 1919-1928 Miladiyya

Sarki Usman ɗan Abdullahi, wanda ake yi wa laƙabi da Usman II. Shi ne Sarki na 52 a jerin Sarakunan Kano, kuma Sarki na 9 a jerin Sarakunan Fulani. Haka kuma shi ne Sarki na biyu da Turawa suka naɗa.

An naɗa Sarki Usman ne bayan ya riƙe Kano na tsawo kwana 40. A lokacin da ya samu sarautar tsufa ta zo masa. A wannan lokaci yana da shekara 76 a duniya.

A zamanin Sarki Usman II, an yi gagarumin taron sarakunan Arewa sakamakon zuwan ɗan Sarkin Ingila wanda ya zo a jirgi. Saboda haka a zamanin Sarki Usman II ne jirgin sama ya fara zuwa Kano. An yi wannan taro a 1925. A kuma zamanin Sarki Usman II aka fara aikin ruwan famfo da na wutar lantarki da kuma gina wasu asibitoci da kuma babban ofishi a cikin birnin Kano. Amma ba a kai ga kammalawa ba rai ya yi halinsa.

Sarki Usman II, ya sarauci Kano na tsawon shekara bakwai da wata biyu a cikin yanayin tsufa da rashin lafiya. Ta-ci-ba-ta-ci-ba, haka ya yi mulkin. Allah Ya jiƙansa da rahama, amin.

Mun ciro wannan rubutu ne daga https://rumbunilimi.com.ng/masarautu.html

Zamu ci gaba

More Stories