✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takarar Musulmi 2 ce ta sa na ki daukar Tinubu a matsayin mataimaki a 2007 —Atiku

Atiku ya ce akwai bukatar yin daidaito a tsarin shugabancin Najeriya.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce takarar Musulmi biyu ce ta sa ya ki amincewa ya dauki Asiwaju Bola Tinubu a lokacin da ya so yi masa takarar mataimaki a 2007.

Atiku, wanda ya shi ne mataimakin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007, ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na ARISE a ranar Juma’a.

sakamakon zamn doya da manja da Obasanjo, Atiku ya fice daga jam’iyyar PDP, inda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a AC.

Sai dai ya kare a matsayi na uku a zaben 2007, wanda marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya lashe, sai Muhammadu Buhari na Jam’iyyar ANPP, da ya kare a matsayi na biyu.

A cikin hirar da Atiku ya yi da ARISE, ya ce tikitin tsayawa takarar Musulmi da Musulmi, wanda ke haifar da cece-kuce a kasar nan a halin yanzu, ya sa ya ki daukar Tinubu a wancan lokaci.

“Ban gamsu da takarar Musulmi da Musulmi ba. Najeriya kasa ce mai kabilu da addinai daban-daban don haka ya kamata a samu daidaito a bangaren addini a cikin shugabancinmu,” in ji shi.

Tinubu wanda zai kara da Atiku a zaben shugaban kasa na 2023, ya zabi Sanata Kashim Shettima, wanda shi ma Musulmi ne a matsayin abokin takararsa, sai dai hakan ya haifar kumfar baki.