✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Takarar Sanata: Ahmad Lawan zai san matsayinsa ranar Litinin

APC ce ta daukaka kara bayan Babbar Kotun Tarayya ta bayyana Machina a matsayin halastaccen dan takara

Kotun koli ta sanya Litinin a matsayin ranar yanke hukunci kan halastaccen dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa a Jam’iyyar APC tsakanin Bashir Machina da Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan.

Jam’iyyar ce dai ta daukaka kara bayan Babbar Kotun Tarayya da ta je ta bayyana Machina a matsayin halastaccen dan takara.

Cikin korfe-korafen jam’iyyar ga kotun ta bakin lauyanta, Sepiribo Peter, akwai batun cewa zaben fidda gwanin ranar 27 ga watan Mayu da ya bai wa Machinan nasara haramtacce ne.

A cewar lauyan, zaben da aka gudanar ranar 6 ga watan Yuni ne halstacce kuma Ahmad Lawan ne ya yi nasara.

Sai dai lauyan Machina, Barista Sarafa Yusuff, ya roki kotun ta yi watsi da bukatar jam’iyyar saboda ba ta da tushe balle makama.

Ya ce har takardar shaida Kwamitin Danjuma Manga da ya gudanar da zaben da Macina ya samu nasara, ya yi wacce ke nuna Sakatariyar APC ta kasa ta ba shi damar gudanar da zaben sanatocin Yobe, tare da wasu mutane biyar.

Alkalin Kotun  Kolin, Centus Nweze, ya dage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Fabrairu domin yanke hukunci.