✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takarar Sanata: Kotu ta umarci INEC ta tabbatar da Akpabio

Babbar Kotun Tarayya ta umarci INEC ta tabbatar da takarar Ministan Neja Delta a kujerar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma

Kotu ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta dawo da sunan Ministan Neja Delta, Godwill Akpabio, a matsayin dan takarar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, na Jam’iyyar APC a zaben 2023.

Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin ne ranar Alhamis bayan hukumar ta cire sunan Akpabio — wanda ya nemi takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC kafin daga baya ya janye — a matsayin dan takarar sanata.

A baya dai jam’iyyar APC ta mika wa INEC sunan Akpabio a matsayin dan takarar Sanatan Akwai Ibom ta Arewa maso Yamma.

Ta kuma mika wa sunan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan — wanda aka kayar a zaben dan takarar shugaban kasa a APC — a matsayin dan takarar Yobe ta Arewa.

Kazalika jam’iyyar ta gabatar da Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi, wanda ya yi zawarcin kujerar shugaban kasa, a matsayin dan takarar Sanatan Ebonyi ta Kudu.

Sai dai kuma a jerin sunayen ’yan takarar da INEC ta fitar babu sunan ko daya daga cikin su hudun.