✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu/Shetima: An Nada Matar Gwamnan Katsina Jagorar Yakin Neman Zabe

An nada mai dakin Gwamnan Katsina, Dokta Zakiyya Aminu Bello Masari, a matsayin Shugabar Mata ta yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyar…

An nada mai dakin Gwamnan Katsina, Dokta Zakiyya Aminu Bello Masari, a matsayin Shugabar Mata ta yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyar APC a 2023, Bola Ahmed Tinubu a jihar.

Hakan dai na cikin wata sanarwa da hadimar gwamnan jihar ta musamman kan yada labarai, Hauwa Ibrahim Jikamshi ta fitar a  ranar Talata.

Ta bayyana cewa nada mai daki gwamnan a wanna matsayi na cikin jerin sunayen mata da aka fitar na  masu yakin neman zaben Tinubu na baya-bayan nan.

“Hajiya Zakiyya ta yi godiya bisa wannan karramawa, tare da yaba wa Jam’iyar APC bisa kokarin da take na inganta lafiyar mata a dukkan matakai, wanda hakan ya sa za su yi tsayuwar daka don ganin Tinubu ya lashe zaben 2023.

“Bayan addu’ar samun zaman lafiya a jihar da Najeriya baki daya, uwargidan gwamnan ta yi kira ga al’umma da su kara mara wa APC baya, domin ci gaba da sharbar romon dimokuradiyya,” in ji Hajiya Hawwa.