Takarar Tinubu: Shugaba Buhari “ya shiga tsaka mai wuya” | Aminiya

Takarar Tinubu: Shugaba Buhari “ya shiga tsaka mai wuya”

Ana ganin ziyarar da Tinubu ya kai wa Buhari a matsayin wata farar dabara
Ana ganin ziyarar da Tinubu ya kai wa Buhari a matsayin wata farar dabara
    Aminiya

Sanarwar jagoran APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu, game da aniyarsa ta neman takarar shugaban kasa ka iya zama kalubale ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Ranar Litinin Tinubu ya tabbatar wa manema labarai aniyar tasa bayan wata ganawa da ya yi da Shugaban Kasar a Fadar Gwamnati ta Aso Rock Villa.

“Na sanar da Shugaban Kasa aniyata, amma ban sanar da ’yan Najeriya ba tukunna, domin har yanzu ina tuntubar [mutane]”, inji Tinubu.

Ziyarar da jagoran na APC ya kai wa Buhari dai na zuwa ne kwana hudu bayan tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci Fadar.

Ana dai ta rade-radin cewa zawarcin Mista Jonathan ake yi ya koma jam’iyyar APC ya yi takarar shugaban kasa a 2023.

Bugu da kari, da wannan sanarwa, akwai yiwuwar sa zare tsakanin Tinubu da yaronsa a fagen siyasa, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, wanda aka yi amanna cewa shi ma yana sha’awar darewa kan kujerar shugaban bayan saukar Buhari.

Gaba kura baya sayaki

Yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a makon jiya dai Shugaba Buhari ya ce ba ruwansa da ko wane ne zai gaje shi a 2023.

Amma kuma ya kara da cewa fitowa ya fadi wanda zai so ya gaje shi ka iya zama barazana ga takarar “magajin” nasa.

A jawabinsa ga manema labarai, Tinubu ya ce bai kayyade adadin mutanen da zai tuntuba ba, amma nan ba da jimawa ba komai zai fito fili.

“Abin kawai da kuke bukatar ji [a yanzu] shi ne waka a bakin mai ita.

“Kun ji gaskiyar magana daga gare ni cewa na shaida wa Shugaban Kasa burina, don haka ba kwa bukatar wata amsa sama da wannan”, a cewar jagoran na APC.

Da aka tambaye shi ko mene ne martanin Buhari, sai Tinubu ya amsa da cewa: “Wannan tsakanina da shi ne. Shi mutum ne mai kaunar dimokuradiyya [don haka] bai ce kada na yi [takara] ba.

“Bai hana ni yunkurin cimma burina ba – wanda buri ne da na jima da shi a raina.

“Me ya sa kuke tunanin zai fadi sabanin haka? Idan kana mulkin dimokuradiyya dole ne ka rungumi manufofi da ka’idoji da tanade-tanaden dimokuradiyya. Fakat”.

‘Babu gudu…’

Sai dai magoya bayan Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo sun ce su ko a jikinsu.

Shugaban wani sashe na kungiyar The Progressive Project (TPP), daya daga cikin kungiyoyin da ke yi wa Osinbajo kamfe, ya ce wannan sanarwa ta Tinubu ba za ta sa su karaya ba.

“Dimokuradiyyar ke nan – Tinubu yana so ya yi takara, mu ma muna so namu gwanin ya yi takara.

“Dadin dimokuradiyya ke nan; muna so namu gwanin ya tsaya takara ne saboda mun yi amanna ya cancanta”, inji Shettima Umar Abba Gana.

Sai dai fa har yanzu Mista Osinbajo bai fito karara ya bayyana burinsa na takarar shugabancin kasa ba.

A cewar Gana, “Osinbajo bai umarce mu mu yi mishi kamfe ba; mu da kanmu muka hadu muke so ya yi takara, muna kuma fata zai fito saboda ingancinsa a matsayin dan Takara”.

Farar dabara

Wani masanin siyasa, Dokta Gbade Ojo, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa Tinubu ya yi farar dabara da ya shaida wa Buhari aniyarsa ta neman takara.

A cewar Dokta Ojo, da faruwar wannan lamari za a fara gwagwarmaya don zabukan 2023 ka’in da na’in.

“Gaskiyar lamari ita ce Tinubu yana so ya shigar da Buhari cikin tafiyarsa.

“Kuma tun da aka shigar da shi, Buhari – mutumin da yake fakewa da cewa shi bai damu da wanda zai gaje shi a 2023 ba – zai san cewa ba zai yiwu ya zama dan kallo ba.

“Dole ne ya yi ruwa da tsaki a batun zabo wanda zai gaje shi ko don samar da kwanciyar hankali a jam’iyyar APC da ma kasa baki daya”, inji Dokta Ojo.

Shi kuwa Farfesa Kamilu Sani Fage na Jami;ar Bayero ta Kano, cewa ya yi wannan sanarwa ta Tinubu bai kamata ta ba kowa mamaki ba, domin ko a 2015 ya so zama mataimakin shugaban kasa.

Sai dai a ra’ayin Farfesa Fage, wannan sanarwa ta Tinubu za ta iya dagula al’amura a jam’iyyar APC “saboda mutane na tunanin cewa tun da Osinbajo yaronsa ne zai mara wa Mataimakin Shugaban Kasar baya. Hakan ne kuma zai fi”.

Ya kara da cewa da ma dai mutanen na zargin Tinubu da taka muhimmiyar rawa wajen mayar da Ofishin Mataimakin hugaban Kasa tamkar wani kango tun 2019, kuma bayyana aniyarsa ta tsayawa takara za ta kara tabbatar da hakan.

“A galibin abubuwan da ya kamata a ce Mataimakin Shugaban Kasa ta jagoranta, irin su yaki da COVID-19, an mayar da shi saniyar ware.

“Sai aka kawo Sakataren Gwamnatin Tarayya, wanda ba zababben jami’I ba ne aka daukaka shi aka ba shi wuka da nama”, inji Farfesa Fage.

Daga nan sai shehin malamin na jami’a ya ce matakin da Tinubu ya dauka zai dusashe burin Farfesa Osinbajo sannan ya dagula siyasar yankin Kudu maso Yamma “saboda akwai mutanen yankin da dama da ba sa son tsohon Gwamnan na Legas.

“…Sai dai idan PDP ta bai wa dan Kudu maso Gabas takara, to watakila Tinubu ya samu goyon bayan masu adawa da shi a yankin Kudu maso Yamma”.

Yayin da 2023 ke kara gabatowa, ’yan Najeriya za su zuba ido su ga yadda za a warware wannan sarkakiya a jam’iyyar APC – musamman ma matakan da Shugaba Muhammadu Buhari zai dauka.