Daily Trust Aminiya - Takardun Pandora: Asirin wasu shugabannin duniya ya tonu

Takardun Pandora

Takardun Pandora: Asirin wasu shugabannin duniya ya tonu

Asirin wadansu shugabanni da attajirai da manyan ’yan siyasa na duniya ya tonu a daya daga cikin manyan bankadar sirri da aka taba samu kan bayanan dukiyarsu.

An bankado bayanan dukiyar shugabannin kasashen duniya 35 na da, da na yanzu da jami’an gwamnatoci fiye da 300 ciki har da wadansu shugabanni a Najeriya da Afirka daga kamfanonin da aka sa a takardun Pandora.

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, kuma Mataimakin Atiku Abubakar a takararsa a zaben 2019 da wani tsohon Babban Jojin Najeriya da wani fasto da wadansu manyan ’yan Najeriya suna cikin wadanda aka zarga da fita da kudaden haram da karya dokoki da boye kadarori ta haramtacciyar hanya.

Sauran wadanda aka fallasa sun hada da Sarkin Jordan da tsohon Firayi Ministan Birtaniya, Tony Blair da Shugaba Vladimir Putin na Rasha da Firayi Ministan Czech, Andrej Babis da sauransu.

Bayanan sun gano cewa Sarkin Jordan ya boye dukiya mai dimbin yawa da kadarori har na Fam miliyan 70 (kimanin Naira biliyan 39.56 a halattaciyar kasuwa ko Naira biliyan 49.35 a kasuwar bayan fage) a kasashen Birtaniya da Amurka.

Takardun sun kuma nuna yadda tsohon Firayi Ministan Birtaniya, Mista Tony Blair da matarsa suka adana Fam dubu 312, a lokacin da suka sayi ofishinsu na Landan.

Bankadar ita ce ta baya-bayan nan a cikin shekara bakwai, bayan na takardun Paradise da Panama da Lud da kuma FinCen.

Fallasar ta alakanta Shugaba Vladimir Putin na Rasha da wasu kadarori a Monaco.

Haka kuma, ta ce Firayi Ministan Czech, Mista Andrej Babis, wanda zabe yake gabansa a makon nan, bai bayyana wata kadararsa ba, wani kamfanin kasar waje da ya yi amfani da shi wajen sayen maka-makan gidaje biyu a Kudancin Faransa.

Mista Duncan Hames, wanda Darakta ne a Kungiyar Transparency International da ke yaki da cin hanci da rashin adalci a duniya, ya ce wahala kullum a kan talaka dai kawai take karewa.

“Idan dan siyasa ya azurta kansa ta hanyar mulki, mutane gama-gari maza da mata ne kawai suke shan wahala kuma kasarsu ke ci gaba da talaucewa.

“A wani lokacin ba ma batun kin biyan haraji ba ne.

“Idan kai ma’aikacin gwamnati ne kuma ka karbi cin hanci domin ka bayar da kwangila ta gina asibiti ga wani naka, hakan ba abin ci gaba ba ne ga kasarka, kuma kasarka za ta wahala saboda cin hancin da ka karba,” inji Mista Hames.

Shugaban Kenya, Mista Uhuru Kenyatta ba a bar shi a baya ba, domin binciken ya gano cewa iyalansa sun mallaki kamfanoni da dama a asirce a kasashen waje.

Cikin kadarorin da suka mallaka har da hannun jari da takardun lamuni na miliyoyin daloli.

Wannan bincike ya gano cewa akwai makusantan Firayi Ministan Pakistan, Mista Imran Khan-ciki har da ministocinsa da iyalansa da suka mallaki kamfanoni na miliyoyin daloli.

Wannan dai ya kasance bincike mafi girma da gamayyar ’yan jarida masu binciken kwakkwafi a duniya suka gudanar inda sama da ’yan jarida 650 suka yi wannan aiki.

Karin Labarai