✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Take-taken da ake nufi da karancin mai da sauya fasalin Naira —Tinubu

Ya ce matsalar karancin fetur ba za ta hana ’yan Najeriya zuwa kada kuri’a ba ranar zabe.

Dan takarar Shugaban Kasa karkashin Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin matsalar karancin mai da ake fuskanta da sauya fasalin wasu takardun Naira da aka yi, take-taken neman wargaza Zaben 2023 ne kawai.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin gangamin yakin neman zaben APC da ya gudana ranar Laraba a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

“Ba sa son zaben ya gudana. So suke su wargaza shi. Za ku bari hakan ta faru?, in ji Tinubu.

Dan takarar ya ce yana da yakinin matsalar karancin fetur ba za ta hana ’yan Najeriya zuwa kada kuri’a ba ranar zabe.

“Sun fara bullo da batun ‘babu mai, kar ku damu, idan babu mai za mu taka da kafa zuwa wajen zabe.

“Idan kun ga dama ku kara kudin mai, ko boye man ko kuma ku canza wa naira launi, za mu ci zabe,” in ji shi.