✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Take-taken Shugaba Buhari na ’yan PDP ne — Masani

Da Sanata Abdullahi Adamu aka kafa jam’iyyar PDP a 1998 da ta mulki Najeriya tsawon shekara 16.

Wani masanin siyasa kuma kwararren mai fashin-bakin kan al’amuran siyasa a Najeriya ya ce wasu daga cikin take-taken Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sun yi kama da na ’yan PDP.

Dokta Abubakar Umar Kari wanda malami ne a Jami’ar Abuja, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da shirin podcast na “Najeriya a Yau” a ranar Litinin wanda ake samu a shafin intanet na Aminiya.

“Ni da ma tun fil azal ina gani APC da PDP ba su da wani bambanci; kawai bambancin [Shugaba Muhammadu] Buhari ne.

“Kuma Buharin ma sannu a hankali shi ma, duk da yake bai taba yin PDP ba, to amma take-takensa irin na ’yan PDP ne”, inji Dokta Kari.

Masanin yana tsokaci ne a kan yadda Shugaba Buhari ya yi uwa ya yi makarbiya wajen zaben Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa da aka yi a bisa doron “maslaha”.

Baya ga kasancewarsa daya daga cikin wadanda suka kafa PDP a 1998 da ta mulki Najeriya tsawon shekara 16, Sanata Adamu ya kuma rike Jihar Nasarawa a karkashin tutar babbar jam’iyyar ta adawa.

Sai dai ya fita daga PDP a 2013 inda ya shiga APC, kasa da shekara daya bayan kafa ta — yana cikin mambobin sabuwar PDP da suka narke suka kafa APC.

Babu maslaha

Dokta Kari ya ce “Kamar dai yadda mu da muke gefe mu ba ’yan APC ko wata jam’iyyar siyasa ba, sai mu ga cewa ba zabe aka yi ba, duk da yake abin da aka yin ba za a ce ya karya doka ba.

“To amma a zahiri ni ina ganin kawai ba a yi wa wannan kalma ta maslaha adalci ba.

“Saboda abin da ya faru shi ne karfa-karfa aka yi da dauki-dora da sunan maslaha.

“Babu wata maslaha tunda a tsarin maslaha ai mutum ne mai yiwuwa za a ba shi baki shi da karan kansa zai ce ‘na hakura a ba wa wani’.

“To amma akasin haka aka samu wajen nadin Sanata Abdullahi [Adamu].

“Domin su abin da suka yi shi ne, tilsta wa sauran masu neman kujerar aka yi kawai su janye takara.

“Kuma hakan yana daya daga cikin abubuwan da suka fito fili ke nan, duk da yake an samu wadansu da suka fito suna jawabi a yayin Babban Taron a kan cewa wadansu shugabanni sun sa baki, ko kuma shugaban kasa ya ce a janye, shi ya sa suka janye.

“To amma idan aka kalli fuskokinsu da muryoyinsu, ni dai a ganina, suna cin karo da kalaman da suke furtawa a baka, kenan ta ciki na ciki, ta baka na baka,” inji malamin.

“Kuma kowa ya sani cewa abin da suke furtawa ba shi ne a cikin zukatansu ba, kawai dai an tilasta musu ne suka yi wannan maslaha.

“Kuma abin da ya sa aka yi, saboda ita maslhan a yanzu ta zama doka ce, wato ita sabuwar dokar zabe ta ce dole sai wanda yake takara ko yake neman takara, idan zai janye sai ya sa hannu, sannan sai ya fito karara ya fada.

“Amma a baya abin da ake yi ai kawai zuwa ake yi a karanto cewa wai an yi maslaha, wanda kuma ba a yi ba, shi kenan sai a fito a karanta cewa ai mutane sun janye ba tare da tuntuba ba, duk da yake a wannan karo an yi tuntuba amma kuma a zahiri tilastawa ce.

Dalilin da aka fifita dora Sanata Abdullahi Adamu a maimakon Almakura

Dokta Kari ya ce, “ni ina ganin dalilai biyu ne — na farko dai wanda mutane da dama suke fada musamman magoya bayan Sanata Abdullahi [Adamu], gaskiya shi ne duk cikin wadannan ’yan takara babu wanda ya kai shi kwarewa a cikin siyasa, babu wanda ya kai shi dadewa a fagen siyasa ana damawa da shi, maganar gaskiya ke nan.

“Saboda haka in dai an bi ta maganar kwarewa da dadewa da damawa a siyasa ya fi karfin Almakura, tun da shi tun cikin 1979 aka fara damawa da shi lokacin da ya je Constitutional Assembly, wato taron nan da ya zana wa Najeriya Tsarin Mulki a 1979.

“A jamhuriyya ta uku ya yi sakatare daga baya kuma shugaban jamiyyar NPN a tsohuwar Jihar Filato, wannan lokaci ba na tsammanin cewa Almakura ya ma kai shekara 20.

“A jamhuriyya ta uku wadda ta daidaice tun kafin ma ta tashi ya nemi takarar gwamna.

“A lokacin mulkin soja ya kuma yi minista, ya rike manyan mukamai.

“A wannan zamanin kuma ya yi gwamna shekara takwas, sannan ya zama shi ne shugaban Kungiyar Gwamnoni na farko.

“Sannan ya yi Sanata tun 2011, saboda haka idan an kawo hanzari cewa kwarewa da dadewa da sanin makama ta siyasa, idan an ce ya fi Almakura ta wannan fuskar zai yi wuya wani ya musanta.

A daya gefen kuma wanda ina ganin shi ne babban dalilin da ya sa aka zabe shi, tun da shugaban kasa ne ya fito fili ya ce shi fa yake so, wato ni ina ganin cewa shugaban kasa yana ganin cewa shi din ne zai masa abin da yake so, shi ya fi yarda da shi, shi hankalinsa ya fi kwantawa a kai, saboda haka duk wani abu da wani zai fada shi ba damuwarsa ba ce, shi dai kawai shi ya yarda da shi, wannan shi ne babban dalili.

Yadda jam’iyyar APC za ta kasance karkashin jagorancin Sanata Abdullahi

Sai dai a yi hasashe, amma dai tun a yanzu sun bar tafarkin dimokuradiyya, don ana ta yin kama karya, ana dauki dora, wasu kungiyoyi da wadansu daidaikun mutane za a iya ma cewa sun fi karfin jam’iyyar.

Saboda haka ni gane nake cewa Abdullahi Adamu ba lallai ba ne ya yarda da wannan, musamman ba mamaki zai sa kafar wando daya da gwamnoni saboda kusan za a ce gwamnoni sun yi babakere a duk harkar jam’iyya da ma harkar siyasar Najeriya.

To ba mamaki za a fara samun takun saka da shi, saboda shi ma tsohon gwamna ne kuma ya san me suke so saboda haka ba lallai ba ne ya yarda da su.

Na biyu kuma kusan za a iya cewa Abdullahi Adamu ya fi kowa sanin matsalolin jam’iyyar APC mai yiwuwa shi ya sa aka nada shi shugaban kwamitin sasanta rigingimu na cikin jam’iyyar.

Ya san rigingimun ya san wu waye suka jawo rigingimun, ya san rigingimun tsakanin wane ne da wane, kuma ni na san cewa zai yi kokarin ganin cewa ya sasanta wadannan rigingimun, amma ba tabbas za a yi nasara.

Abin da kuma na sani shi ne Abdullahi Adamu mutum ne wanda ya bi ma bakinsa, kuma mutum ne wanda idan ya kalli gaba bai waiwayawa, bai jin tsoron ya yi magana koda mai daci wacce za ta bata ran mutane, ko kuma shi ya kan nuna cewa ya fi kowa biyayya ga shugaban kasa, saboda haka abin da zai shi ne zai biya muradun wadanda suka kawo shi.