Takunkumin da aka sa mana ne silar tsadar abinci a duniya – Rasha | Aminiya

Takunkumin da aka sa mana ne silar tsadar abinci a duniya – Rasha

Kakakin Ma`aikatr Wajen Rasha Maria Zakharova
Kakakin Ma`aikatr Wajen Rasha Maria Zakharova
    Rahima Shehu Dokaji

Kasar Rasha ta ce karairayi kawai kasashen yammacin duniya ke yadawa kan abubuwan da ke haddasa karanci da tsadar abinci a duniya.

Kakakin Ma’aikatar wajen Rasha, Maria Zakharova, ce ta bayyana hakan ranar Laraba a babban Birinin Rasha wato Moscow.

Ta ce abin da ke haddasa karancin abinci a duniya bai wuce takunkumin da kasar Amurka da kungiyar Tarayyar Turai suka kakaba wa Rashan ba dalilin mamaye Ukraine da kasar ta yi.

Ta ce ba ya ga asarar rayuka da barnar da mamayar Rasha ta haifar, yakin da kuma yunkurin Turan na durkusar da tattalin arzikin kasar ya sanya farashin hatsi da man girki da taki da ma makamashi ya ci gaba da tashin gwauron zabo a duniya.

Ta sanar da manema labarai cewa ta kadu da furucin da kasashen yamman ke yi na dora alhakin karancin abincin kacokan kan Rashan.

Ta ce: “wato yanzu kasashen yamma za sui ya ba wa Ukraine dukkanin wadannan makaman, amma saboda wasu dalilai su gaza fitar da komai daga Ukraine din”?

A ranar tara ga watan Yuni ne dai Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy ya yi gargadin cewa miliyoyin mutane za su fuskanci yunwa saboda toshe tashar jirgin ruwa ta Black Sea da Rashan ta yi, wanda ya bar duniya a mummunar matsalar abinci.

Kasashen biyu da ke yaki da juna wato Rasha da Ukraine sune giwayen duniya a samar da kayan abinci na gona, inda Rashan ke gaban Ukraine a matsayin wacce ta fi kowacce kasa noman Alkama, yayin da Ukraine kuma ta fi kowacce fitar da irin Sun Flower.

Kazalika Zakharova ta ce: “Babu hikima a abin da Kungiyar Taryyar Turan ke yi na cewa  an haifar da matsalar rashin abinci, yayin da ita kuma ta toshe hanyoyin isar da kayayyaki gare su da nahiyarsu baki daya”.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ayyana yakin a matsayin na tayar da kayar baya ga Amurka, wacce ya ce ta kaskantar da Rashan tun bayan faduwar Tarayyar Soviet a shekarar 1991 ta hanyar tura sojojin Nazi zuwa yamma.