✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Talakawa a yi wa Gwamnatin Buhari uzuri

Salam Edita don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci dangane da kama mulkin Buhari. Tabbas talakawan Najeriya sun dade suna mafarkin zuwan mulkin…

Salam Edita don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci dangane da kama mulkin Buhari. Tabbas talakawan Najeriya sun dade suna mafarkin zuwan mulkin Buhari, saboda kyakyawan zaton samun saukin badakalar da aka dade ana tafkawa a Najeriya, musamman matsalar cin hanci da rashawa. Hakan ne ya sa talakawa suka fito kwansu da kwarkwata a ranar zabe, suka kada wa Buhari ruwan kuri’u, tare da tsare akwatinansu, har ma da raka su wajen tattara sakamakon zaben hakika talakawa sun yi ruwa da tsaki wajen ba da kyakkyawar gudunmawa a lokacin yakin neman zabe tabbas kungiyoyi da dama sun taka rawar gani, musamman kungiyoyin da ke da kusanci da fararan hula haka kuma daidaikun mutane sun yi rawar gani, ta hanyar amfani da yanar gizo, wato hanyoyi Face book,Twiter da sauransu.
Buhari ya hau mulki kwanaki 100 da ya yi mutane sun ka sa kunnuwansu suna so, su ji wasu alkawuran da za su yi dariya, amma sai suka ji akasin haka. To, amma ni a fahimtata mu talakawa muna mantawa da kaddara. Haka kuma muna mantawa da hukuncin Allah da yadda shugaban ya samu kasar, domin kuwa ya samu kasar ne cikin badakaloli iri-iri tsawon shekaru  da suka yi wa kasar nan katutu, duk wadannan abubuwan mutane ba sa dubawa kawai abin da suke jira yanzu-yanzu wannan kuma sai Allah. Su kuma ‘yan adawa sun shiga cikin mutane suna ta zuga su cewar, wai dama haka mulkin Buharin yake ai gwara mulkin baya. Hakika wannan ba karamin kuskure bane. Don haka ina bai wa talakawa ’yan uwana shawara ya kamata a yi wa wannan gwamnatin uzuri, tunda har yanzu ba ta gama zama sosai ba. Ministoci ma ba su fara aiki ba, kuma har yanzu gwamnatin ba ta yi kasafin kudinta ba. Ya kamata a cigaba da taimaka wa wannan gwamnati da addu’a, ita ce kawai hanyar da ta dace. Daga Aminu Abdu Baka Noma Sani Mai Nagge PRO. Muryar Talaka, reshen Jihar Kano 08069735151-08028505350