✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talauci Ne Musabbabin Tabarbarewar Tsaro —Zulum

Gwamnatin Jihar Borno ta rufe sansanonin ’yan gudun hijra hudu, tare da raba wa mutane 11,000 da ke cikinta gidaje kyauta

Gwamnatin Jihar Borno ta rufe sansanonin ’yan gudun hijra hudu, tare da raba wa mutane 11,000 da ke cikinta gidaje kyauta a kauyuka shida.

Da yake rufe sansanonin a ranar Alhamis, Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya ce ya yi hakan ne sakamakon dawowar zaman lafiya a jihar.

Ya ce baya ga hakan, yana fargabar kuncin rayuwar da ’yan gudun hijirar ke ciki ya sanya su hadewa da ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP.

A don haka ya ja hankalin Gwamnatin Tarayya da ta kawo karshen talaucin da ke addabar al’umma, domin shi ne kadai maganin tabarbarewar tsaron Najeriya.

“Ba mun sallami ’yan gudun hijirar ba ne kawai, mun hada musu har da jarin da za su dinga samun kudaden shiga, da Naira dubu 100 kowanne, sannnan kuma za mu raba musu kayan abinci daga kudin tallafin da muka ware domin kula da su.

“Hanyar da kadai za a kawo karshen tabarbarewar tsaro ita ne magance tushenta wato talauci, da matsalolin yanayi, da karancin ababen more rayuwa a kasa.

“Saboda haka mu a bangarenmu abin da muka yi shi ne mayar da ’yan gudun hijirar nan muhallansu cikin mutunci, kuma za mu ci gaba da hakan, har sai mun tabbatar kowa ya samu [muhalli]”, in ji Zulum.

A karshe ya yabawa Shugaban Kungiyar Tallafa Wa Wadanda Iftila’i Ya Same su, Janar Theoplilus Danjuma mai ritaya bisa tallafawa ’yan gudun hijirar da muhallai na tsawon shekaru 13.