✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talauci ya sa sojoji yin jigilar fasinja da jiragen yaki

Fiye da rabin mutanen kasar sun fada cikin kamfar talauci.

Tabarbarewar tattalin arzikin Lebanon ya tilasta sojojin kasar jigilar fasinja da jiragen yaki domin samun kudin da za su rika kula da su.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito Kakakin Sojin Lebanon, Kanar Hassan Barakat yana cewa “Yakin da muke ciki a yanzu na tabarbarewar tattalin arziki ne, don haka akwai bukatar mu nemo wata hanyar… abin da muke yi shi ne mu rika jigilar fasinjoji da helikwaftocinmu.”

Ya kara da cewa, “Kudin da ake biya don wannan jigila sun isa a kula da jiragen.”

Ana biyan Dala 150 (kimanin Dala dubu 75) don yin tafiyar minti 15 a jiragen bayar da horon soji samfurin Robison R44.

Lebanon dai tana fama da matsin tattalin arzikin da Bankin Duniya ya bayyana da daya daga cikin mafiya muni a tarihin wannan zamani.

Darajar kudin kasar ta fadi da fiye da kashi 90 cikin 100 a kasa da shekara biyu, sannan fiye da rabin mutanen kasar sun fada cikin kamfar talauci.

Kwamandan Sojin Kasar, Janar Joseph Aoun ya yi gargadi a watan jiya cewa, rikicin da muguwar almundahana ta haifar a shekarun da suka gabata da kuma barnar kudi da gwamnatoci suka yi, suna iya jawo rugujewar dukkan cibiyoyin gwamnati ciki har da soji.

A cewarsa, darajar albashin soja a wata yanzu Dala 90 ne (kimanin Naira dubu 43).

Lebanon ce ta fi kowace kasa samun tallafin soji daga Amurka, kuma sojojin suna ta kokarin tabbatar da zaman lafiya a Lebanon tun kawo karshen Yakin Basasar 1975 zuwa 1990.

A tsakiyar wannan wata ne kasar Katar ta bayar da sanarwar za ta tallafa wa sojin Lebanon da tan 70 na kayan abinci a kowane wata.

Wani mai suna Adib Dakkash mai shekara 43 da ya kai ziyara daga kasar Switzerland, ya ce, “Abin jin dadi ne ’ya’yana su ga Lebanon da kyakkyawan yanayin Lebanon ta sararin samaniya daga cikin jirgin.

“Na gwammace in kashe Dala 150 jirgin helikwafta na soji ya ci gaba da aiki ta yadda matuka jiragen za su ci gaba da aiki, maimakon in kashe kudi a otel wajen cin abinci ko sayen wasu kayayyaki marasa amfani.”