✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta fice daga yarjejeniyar zaman lafiya a Pakistan

TTP ta yi watsi da yarjejeniyar da aka kulla kan zargin gwamnatin Pakistan ta karya alkawari.

Kungiyar Taliban ta kasar Pakistan (TTP) ta yi fatali ta yarjejeniyar tsagaita wuta da ta kulla da gwamnati domin samun zaman lafiya a kasar.

Tun da farko kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan ce ta sa baki aka kulla yarjejeniyar, kafin daga bisani TTP ta yi watsi da shi, kan zargin gwamnatin Pakistan ta karya alkawari.

Kungiyar na zargin sojoin gwamnati da kashe mata mayaka da kuma saba sharuddan yarjejeniyar da bangarorin suka dauka, wanda wa’adinsa ke karewa a watan Disamban da muke ciki.

“Ba zai yiwu a tsawaita wa’adin yarjejeniyar ba a irin wannan yanayi.

“Yanzu kuma sai al’ummar Pakistan su yi wa kansu alkalanci a kan wanda ke saba alkawari,” inji sanarwar da kungiyar ya fitar.

TTP mai akidu irin na takwararta ta Afghanistan ta fara tayar da kayar baya a Pakistan ne a shekarar 2007 ne bayan an kafa kungiyar.

Bayan shekara bakwai da murkushe ta, a halin yanzu gwamnatin Pakistan na kokarin dakile farfadowarta bayan Taliban a makwabicyar kasar, Afghanistan ta karbe mulki.

A karkashin yarjejaniyar tsagaita wutar da TPP da gwamnatin Pakistan suka kulla ne gwamnatin kasar ta saki mayakan kungiyar 100 da take tsare da su.

A ranar Juma’a, wani jami’in gwamnati ya ce, “Mun yi mamakin sanarwar da kungiyar ta fitar bayan ta sun ba wa wakilanmu tabbacin tsawaita wa’adin tsagaita wutar.”

A watan Oktoba ne Fira Minista Imran Khan ya sanar cewa gwamnatinsa na tattaunawa da kungiyar a karon farko tun 2014, da taimakon kungiyar Taliban da ta kafa gwamnati a Afghanistan.

Gwamnatocin Pakistan sun ce rikicin TTP ya yi ajalin akalla mutum 70,000 baya ga hare-hane a makarantu da wuraren ibada da kasuwanni da otal-otal a ssassan kasar.