✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta haramta wa Mata balaguro ba muharrami

Taliban ta ci gaba sanya dokoki a Afghanistan tun bayan da ta karbe iko watan Agusta.

Kungiyar Taliban wadda ta kafa gwamnati a kasar Afghanistan, ta haramta wa mata yin doguwar tafiya ba tare da rakiyar wani muharrami ba wato miji ko dan uwa namiji na kusa.

Hakan dai na kunshe cikin wani sabon tsari da gwamnatin Taliban ta fitar a ranar Lahadi, a yunkurinta na kare hakkin mata da suka tashi yin doguwar tafiya.

Sanarwar da ma’aikatar kula da al’amuran addini ta fitar ta ce za a sahale wa mata iya yin gajeran balaguro ne kadai ba tare da muharrami ba kwatankwacin tafiyar kilomita 72.

Karkashin sabbin tsare-tsaren gwamnatin Taliban ta kuma sahale wa mata masu motar kansu su iya tuka kansu don yin zirga-zirga a cikin gari amma dole sai suna sanye da cikakken hijabin musulunci.

Haka kuma an umarci dukkanin masu ababen hawa daga yanzu kada su sake daukar duk wata mata sai wadda take sanye da hijabi.

Wannan mataki dai na zuwa ne makonni kalilan bayan Taliban ta umarci gidajen talabijin na kasar su daina haska wasanni dirama ko kuma tallace tallacen da ke dauke da mata a ciki.

Haka zalika karkashin dokokin Taliban wajibi ne matan da ke aiki a gidajen talabijin su sanya cikakken hijabi lokacin da suke gabatar da shirye-shiryensu ba tare da nuna fuskarsu ba.

An rushe Hukumar Zaben Afghanistan

A karshen makon da muka yi bankwana da shi ne Taliban ta rusa hukumar zaben kasar Afganistan, wadda ta shirya tare da sa ido kan zabukan da suka gudana a zamanin gwamnatin da ta gabata, wadda kasashen yammacin Turai ke marawa baya.

Da yake  sanar da matakin a ranar Asabar, kakakin gwamnatin Taliban Bilal Karimi ya ce, a halin yanzu babu bukatar ci gaba da wanzuwar hukumar zaben Afghanistan tare da wasu makamantanta, wato hukumar da ke karbar korafe korafen zabe mai zaman kanta ta kasar.

A tsakiyar watan Agustan da ya gabata ne kungiyar Taliban ta sake mamaye madafun ikon kasar a daidai lokacin da Amurka ta fara janye dakarunta da suka shafe shekaru 20 su na yaki da Taliban da kuma ’yan ta’adda na kungiyar IS.