✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Taliban ta kafa sabuwar gwamnati a Afghanistan

Sabuwar gwamnatin za ta kasance karkashin Mohammad Hasan Akhund.

Kungiyar Taliban ta sanar da kafa sabuwar gwamnati a kasar Afghanistan wacce za ta kasance karkashin jagorancin Mohammad Hasan Akhund.

Abdul Ghani Baradar kuma shi ne zai kasance Mataimakin Shugaban Kasa, yayin da Sirajuddin Haqqani zai kasance sabon Ministan Cikin Gida, kamar yadda kakakin kungiyar, Zabihullah Mujahid ya sanar yayin wani taron manema labarai a ranar Talata.

Bugu da kari, Taliban ta kuma nada, Mullah Mohammad Yaqoob, da ga Mullah Omar wanda ya kirkireta a matsayin sabon Ministan Tsaro.

Hedayatullah Badri kuma shi ne zai kasance mai rikon mukamin Ministan Kudin kasar.

Sabon Shugaban Kasar dai, Mohammad Hasan Akhund ya taba zama mataimakin Firaminista a gwamnatin kungiyar ta baya, tsakanin shekarar 1996 zuwa 2001.

Akasarin sabbin jami’an gwamnatin kasar da aka sanar dai sun taba rike mukamai a tsohuwar gwamnatin kasar kafin a hambarar da ita daga mulki.

Kakakin na Taliban ya kuma ce gwamnatin za ta kasance ta rikon kwarya ce kuma za ta yi kokarin zakulowa tare da tafiya da sauran mutane daga wasu sassan kasar.

Kungiyar Taliban dai ta kwace mulkin kasar Afghanistan a watan da ya gabata kuma tun a lokacin da kasar Amurka ta kammala yanjewa daga kasar ake ta tsammani sanarwar kafa sabuwar gwamnatin.

Sun sha alwashin kafa gwamantin da za ta tafi da kowa ta hanyar nada dukkan kabilun kasar, ko da yake ba lallai ta kunshi mata ba.