✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta murkushe gyauron masu yi mata tawaye

Dakarun tsohuwar gwamnati da suka ja daga a yankin Panjshir sun mika wuya.

Kungiyar Taliban ta ce ta kwace yankin Panjshir, wanda shi ne tushen inda ta samu turjiya na karshe a kasar Afghanistan.

Kungiyar Taliban ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.

Wasu kungiyoyi masu adawa da kungiyar ta Taliban da burbushin dakarun tsohuwar gwamnatin kasar, a karkashin tutar National Resistance Front (NRF), suka ja daga a yankin suka ki mika wuya ga Taliban din.

“Da wannan nasara, yanzu an kammaka ceto kasarmu daga yanayin gaba-kura-baya-sayaki da yaki ya jefa ta a ciki”, inji kakakin Taliban Zabihullah Mujahid.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, ya ruwaito cewa wannan na faruwa ne a daidai lokacin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka ke kan hanyarsa zuwa birnin Doha na kasar Qatar don gano bakin zaren rudanin da janyewar sojojin Amurka ta haddasa a Afghanistan.

Tun da maraicen ranar Lahadi, gamayyar ta NRF ta bayyana shan mummunan kashi a fagen yaki sannan ta yi kira da a tsagaita bude wuta.

Gamayyar ta kunshi mayakan yankin masu biyayya ga Ahmad Massoud — dan fitaccen kwamandan nan da ya yaki Tarayyar Soviet da kungiyar Taliban, Ahmad Shah Massoud — da dakarun tsohwar gwamanti wadanda suka tsere zuwa yankin na Panjshir.