✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta soma biyan albashin ma’aikata a Afghanistan

Za a soma biya dubban ma’aikatan da suke bin albashi hakkinsu daga yau Asabar.

Gwamnatin da Taliban ta kafa a Afghanistan ta bayyana shirinta na soma biya dubban ma’aikatan da suke bin albashi hakkinsu daga yau Asabar.

Tun bayan da Kungiyar Taliban ta kwace ikon Kasar Afghanistan a watan Agusta, ma’aikatan gwamnati a kasar ba su karbi albashinsu.

Jaridar Punch ta ruwaito wani mai magana da yawun Ma’aikatar Kudi, Ahmad Wali Haqmal ya shaida cewa za a biya albashin ma’aikatan na wata uku, sai dai bai yi karin haske ba kan daga inda za a samu kudin ba.

Rahotanni sun ce Jamus da Netherlands sun bayyana cewa sun kudiri aniyar biyan ma’aikatan lafiya da na ilimi kai tsaye ta hanyar kungiyoyi masu zaman kansu.

Tun bayan da kungiyar ta kwace iko a kasar ce Kasashen Yamma suka dakatar da asusun Afghanistan mai dauke da biliyoyin daloli.