✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta wajabta wa mata sanya nikabi a Afghanistan

Ko kafin dokar dama akasarin matan kasar na sanya nikabin

Gwamnatin Taliban a kasar Afghanistan ta bayar da umarnin cewa dole mata su rika sanya nikabi su rufe fuskarsu yayin shiga cikin jama’a.

Kazalika gwamnatin ta yi gargadin cewa akwai hukunci a kan muharramin duk macen da ta ki bin umarnin.

Tuni wannan umarni ya janyo suka daga Majalisar Dinkin Duniya da masu fafutika da kuma kasashen yammacin duniya.

Wani bincike da aka yi ya gano cewa kashi 99 cikin 100 na matan kasar suna rufe fuskokinsu, don haka gwamnatin ta bayar da umarnin ne ga ragowar kashi
daya na matan da ba sa sanya nikabin su rufe fuskarsu.

A watanni tara da suka wuce, an bai wa mata shawarar sanya hijabi su rufe jikinsu a kasar.

Yawanci matan da suke zaune a biranen kasar ne ba sa sanya nikabin, don haka
wannan doka za ta fi shafar su.

Tuni dai masu fafutika musamman mata su soki matakin suna masu cewa
sanya hijabi ko nikabi ba shi ne zai canja mace ba, shiriya a zuci a take.