✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta zartar da hukuncin kisa a bainar jama’a a Afghanistan

Mahaifin wanda aka kashe aka ba bindiga ya harbe mutumin

A karon farko tun bayan dawowarta mulkin kasar Afghanistan a bara, gwamnatin Taliban ta aiwatar da hukuncin kisa a bainar jama’a kan wani da kotu ta samu da laifin kisan kai.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ranar Laraba na nuna niyyar gwamnatin Taliban ta jaddada amfani da tsarin shari’ar Musulunci a kasar kamar yadda ta yi a baya zamanin mulkinta a shekarar 2001.

An dai zartar da hukuncin ne a lardin Farah ta hanyar harbe mutumin da bindiga, wanda aka ba mahaifin wanda aka kashe ya yi, a gaban daruruwan masu kallo da kuma jami’an Taliban din da dama, kamar yadda Kakakin gwamnatin kasar, Zabihullah Mujahid ya sanar.

Ya ce wasu daga cikin jami’an gwamnatin sun taso ne takanas tun daga Kabul, babban birnin kasar, don shaida zartar da hukuncin.

Zabihullah ya ce sai da dukkan manyan kotunan kasar uku da babban jami’in gwamnatin Taliban, Mullah Haibatullah Akhunzada, suka amince da aiwatar da hukuncin kafin a yanke shi.

Mutumin da aka yanke wa hukuncin mai suna Tajmir dai tun da farko an same shi ne da laifin kashe wani mutum shakara biyar da suka gabata, sannan ya sace masa babur da waya.

Mutumin da aka kashe a wancan lokacin an ce sunansa Mustafa, kuma mazaunin lardin Farah ne.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana ko wanda aka zartarwa da hukuncin ya amince da aikata laifin a gaban kotun ba, ko kuma a’a.

Zabihullah dai ya ce mahaifin wanda aka kashe kuma aka yi wa satar sai da ya harbi mutumin da aka aiwatar wa da hukuncion kisan har sau uku da bindiga a ranar Laraba.