✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin kudin mota ba daidai yake da tallafin mai ba

Bayar da tallafin N5,000 ga iyalai miliyan 40 abin kunya ne

Ranar Larabar da ta gabata ’yan Najeriya suka wayi gari da shaida kashi na biyu, fitowa ta farko, a wasan kwaikwayon da aka jima ana yi a fagen mulkin kasarsu game da tallafin man fetur.

A wannan sabon kashin, Gwamnatin Tarayya ce ta bayyana cewa daga watan Yunin 2022 za ta maye gurbin tallafin man fetur da tallafin kudin mota ga iyalai miliyan 40 na tsawon wata shida zuwa wata 12, lokacin da farashin man zai kai Naira 340 a kan ko wacce lita.

Gwamnatin ta kare wannan mataki da kafa hujjar cewa da ma tanadin yin hakan yana kunshe a cikin Dokar Harkar Fetur da aka sanyawa hannu kwanan nan, wadda kuma za ta fara aiki a watan Yunin badi.

Ta kuma kafa hujja da cewa kashe makudan kudi – abin da yanzu ya kai Naira biliyan 243 duk wata, ya kuma lakume Naira biliyan 864 a wata tara na farkon shekarar 2021 – a matsayin tallafin mai ba abu ba ne mai dorewa, don haka dole a yar da kwallon mangwaro ko a huta da kuda.

Gwamnatin ta yi gargadin cewa gazawa wajen janye tallafin man zai janyo wa baitul malin kasa asarar Naira tiriliyan 3 duk shekara, lamarin da ka iya sanya kamfanin mai na kasa, NNPC, ya kasa ajiye ko sisi a lalitar Gwamnati bayan biyan tallafin.

‘Gwamnoni na goyon baya’

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya amsa amon wannan ikirari lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da wani rahoto na Bankin Duniya, yana cewa gwamnoni suna goyon bayan wannan mataki saboda idan ba a janye tallafin mai ba, jihohi 35 ba za su iya biyan albashin ma’aikata ba a badi.

’Yan Najeriya da dama sun dade da rungumar kaddara game da yiwuwar janye tallafin man fetur watan-wata-rana tun kafin Kudurin Dokar Harkar Man Fetur (PIB) ya zama doka.

Sai dai yadda zai haifar da karuwar farashin mai da kashi 200 cikin 100 lamari ne da zai haifar da mummunan tashin farashin kayayyaki da kazamar hauhawar farashi a daidai lokacin da tuni miliyoyin ’yan Najeriya ke dandana kudarsu sakamakon karuwar farashin kayan abinci.

Wacce irin ukuba ake so sai ’yan Najeriya sun dandana sakamakon gazawar Gwamnati wajen tafiyar da tallafin mai yadda ya kamata?

Da ma tsadar abinci, da iskar gas, da icen girki, da gawayi, da sauran kayayyakin da iyalai ke bukata don su rayu, ta gallabi ’yan Najeriya, tana kara dilmiya su cikin talauci da fatara.

Amma Gwamnati na nuna yatsa ga wadannan ’yan Najeriya tana zargin su da lakume kudaden da take samu da sunan tallafin man fetur.

Kudin gudanar da gwamnati

Gwamnatin ba ta damu ba da makudan – kai, kazaman – kudin da take kashe wa kanta duk shekara da sunan “kudin gudanarwa”.

Misali, ko da ba a saka abin da za a kashe a kan tallafin mai a kasafin kudi na 2022 ba, Gwamnati ta kasafta wa kanta Naira tiriliyan 6.83 da sunan kudin gudanarwa – wato kudaden albashi da gudanarwa ta yau da kullum kadai.

Kashi 41.7 cikin 100 ke nan na kasafin na Naira tiriliyan 16.39, wanda ya haura na kasafin 2021 da kashi 18.5 cikin 100.

Hakan na nufin a shekarar da Gwamnati ke ce wa ’yan Najeriya su yi damara don fuskantar janye tallafin mai, ita tana shirin kashe wa kanta karin kudi a kan wanda ta kashe a baya.

Don haka muke ganin cewa a maimakon Gwamnati ta kakaba wa ’yan Najeriya, wadanda tuni aka talauta su, dukkan nauyin da ke tattare da tallafin mai, kamata ya yi ta nemo wadansu hanyoyi da akalla za a ‘raba asara’.

Idan Gwamnati za ta rage kudaden gudanarwarta a kasafin kudi na badi, ko da da kashi 10 cikin 100 ne, to za a samu akalla Naira miliyan 700 da za a iya biyan tallafin mai da su daga watan Yunin 2022.

Hakan mai yiwuwa ne duba da almubazzaranci da barnar da masana suka nuna a kasafin kudi na 2022.

Wannan ne ya kawo mu ga tallafin kudin mota Naira 5,000 ga iyalai miliyan 40, wadanda su ne kashi 40 cikin 100 na can kasan ma’aunin talauci, kamar yadda Ministar Kudi ta ce.

Babban abin kunya

Abin kunyar da ke tattare da wannan shiri, idan Gwamnati na so a fada mata gaskiya, ba kawai kankantar wannan kudi (Naira 5,000) ga iyali guda a duk wata ba ne – babban abin kunyar shi ne cewa akwai iyalai miliyan 40 a Najeriya da ke bukatar irin wannan tallafi da bai taka kara ya karya ba.

Duba da yawan mutanen da ke rayuwa a galibin gidajen Najeriya, ko da iyalai miliyan 20 aka ce to ana maganar mutum kusan miliyan 80 ke nan.

Idan har Gwamnati na bukatar tallafa wa iyalai har miliyan 20 da Naira 5,000 kacal duk wata don su kai labari, to ba ta bukatar wata shaida ta daban cewa manufofinta na tattalin arziki ba sa aiki yadda ya kamata wajen raba ’yan Najeriya da talauci.

Bugu da kari, ta yaya Gwamnati take fatan aiwatar da shirin?

Duba da yadda zarge-zargen almundahana suka dabaibaye shirin samar da ayyuka na N-Power, da rabon tallafin COVID-19, da sauran shirye-shiryen rarraba kudade ga talakawa da wannan Gwamnatin ta kirkiro a baya, fatan cewa wannan shirin na bai wa talakawa tallafin kudin mota zai kai ga wadanda za a yi domin su kadan ne.

Ko da kuwa Gwamnatin ta yi nasarar gano mutanen da suka fi talauci yadda ya dace.

Hakan kuwa na nufin mafiya talauci a tsakanin ’yan Najeriya za su dandana wahalar janye tallafin mai rubi biyu ke nan.

Kari a kan wannan, mun lura, cikin matukar damuwa, cewa alal hakika fikirar wannan kuduri ta samo asali ne daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya duk da cewa Gwamnati na ikirarin cewa tunaninta ne.

Ba a fi mako biyu ba, IMF ya fitar da wani rahoto yana bai wa Gwamnatin Najeriya shawara ta janye tallafin mai.

Sannan a makon jiya Bankin Duniya ma ya bi sahu da wani rahoto makamancin wancan.

‘Ba mu yarda ba’

Takamaimai saboda irin wannan tsoma bakin a manufofin mulki ne mutane da yawa suka bai wa Gwamnatin Najeriya shawara da ta yi ta-maza ta juya baya ga rancen IMF da Bankin Duniya.

Amma a wannan karon abin ya fi muni saboda a daidai lokacin da IMF da Bankin Duniya ke bai wa Gwamnatin Najeriya shawara ta kara tsunduma miliyoyin ’yan kasa cikin ramin talauci ta hanyar janye tallafin man fetur, mutane a Turai da Amurka na amfana da tallafi iri-iri da taimakon tsabar kudi daga gwamnatocinsu don rage radadin Annobar COVID-19.

Muna mamakin yadda ake so a ce sai ’yan Najeriya sun sha bamban.

Dadin dadawa, muna mamakin yadda Gwamnatin Najeriya ba za ta dogara da masana tattalin arziki ’yan kasa ba don samun shawara a kan yadda za a tsara dabarun cikin gida don magance matsalolin gida.

Don haka, mun bi sahun kungiyoyin kwadago na kasa, da dalibai, da miliyoyin ’yan Najeriya wajen cewa ba mu yarda da karin farashin mai ba ta ko wacce siga.

Idan akwai bukatar Najeriya ta matse bakin aljihu, to Gwamnati ce ya kamata ta zama abar kwaikwayo.