✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin Mai: Za a binciki zargin karkatar da Dala biliyan 7 a gwamnatin Buhari

Za a yi binciken ne tsakanin 2017 zuwa 2021

Majalisar Wakilai ta kafa kwamitin wucin-gadi domin binciken yadda aka gudanar da biyan kudaden tallafin man fetur a karkashin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Majalisar dai ta bukaci kwamitin da ya fara gudanar da binciken tun daga shekarar 2017 har zuwa 2021.

Bukatar hakan ta biyo bayan amincewa da wani kuduri da dan majalisa Sergius Ose daga jihar Ogun ya gabatar a zauren majalisar ranar Laraba.

Da yake gabatar da kudurin, dan majalisar ya bayyana damuwa kan zargin da ya yi cewa kamfanin mai na NNPC da wasu masu ruwa da tsaki kan harkar man fetur a Najeriya sun sa ya zuwa karshen 2021, kasar ta tafka asarar sama da Dalar Amurka biliyan bakwai a cikin sama da ganga miliyan 120 da aka sayar.

Ya kuma ce akwai hujjojin da ke nuni da cewa ana yin aringizo a cikin kudin na tallafin mai, sabanin abin da yake a zahiri na ainihin yawan man da ake sayarwa a kullum da ya haura Naira tiriliyan biyu.

Ya ce kudaden da NNPC da sauran abokan huldarsa suke aringizon nasa a kullum sune Naira 37 zuwa 39 kan kowacce lita, wanda jimlarsa ke kaiwa Naira biliyan 70 a kowanne wata, wato Naira biliyan 840 a shekara.

Da yake tsokaci a kan kudurin, Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, ya bayyana kudurin a matsayin muhimmi, inda ya ce batun biyan kudaden tallafin mai ya dade yana ci wa Najeriya tuwo a kwarya.

Daga nan sai ya umarci Mataimakinsa da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar da kuma Bulaliyarta da su fito da kwakkwaran kwamitin da zai binciki zarge-zargen da kudurin ya yi.