✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin man fetur na lakume N120bn a duk wata

Ba za mu iya ci gaba da biyan kudin tallafin ba, inji NNPC

Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), ya ce gwamnati na kashe Naira biliyan 120 a kowane wata wajen biyan tallafin man fetur.

Shugaban NNPC, Meke Kolo Kyari ne ya bayyana hakan yana mai cewa, kamfanin ba zai iya ci gaba da daukar nauyin biyan kudin tallafin man da a halin yanzu ake sayar da lita a kan N162 ba.

Ya ce kudin shigo da fetur har a karasawa da shi zuwa gidajen mai na kamawa ne a kan N234 kowace lita, amma gwamnati ta sa ana sayarwa a kan N162.

Shugaban na NNPC ya ce a duk wata abin da ake kashewa domin biyan abin da gibin farashin ya samar na kaiwa tsakanin Naira biliyan 100 zuwa biliyan 120.

Mele Kyari ya ce NNPC ke daukar nauyin biyan tallafin bambancin ake kuma sanyawa cikin bayanan kudaden da kamfanin ke kashewa.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, a lokacin taron Kwamitin Ministoci karo na biyar, inda ya ce, kamata ya yi a bar wa ’yan kasuwa harkar su rika sayar da mai gwargwadon yadda kasuwa ta kama.

Ya yi bayanin ne bayan Minista a Ma’aikatar Albakatun Mai, Timipre Sylva, ya yi karin haske kan fadi-tashin da ake yi na ganin an aiwatar da Kudurin Dokar Mani ta PIB.