✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin man fetur ya lakume Naira biliyan 864 a wata 8

Ana ta muhawara a kan ko ya kamata a janye tallafin mai a Najeriya

Kamfanin Man Fetur na Kasa, wato NNPC, ya kashe Naira biliyan 864 a kan tallafin man fetur a cikin wata takwas bana.

Da kamfanin na NNPC bai samar da wannan tallafi ba, da an danka kudin ga Hukumar Rarraba Kudin Shiga ta Tarayya (FAAC).

A asusun FAAC ne dai hukumomin gwamnati masu samar da kudin shiga kan saka abin da suka tara, ciki har da cinikin danyen man fetur da haraji da kudin fito, da sauransu.

Najeriya na tsaka mai wuya ta fuskar tattalin arziki yayin da ake ci gaba da tafka muhawara a kan ya kamata a janye tallafin mai ko bai kamata ba.

A janye ko a’a?

Manazarta da dama da hukumomin kasa-da-kasa dai sun sha kira da  a janye tallafin saboda yana lakume makudan kudaden da ya kamata a yi amfani da su don bunkasa tattalin arzikin kasa da kawar da talauci.

A halin yanzu dai kasar na amfani da kudin da ta samu bayan ta sayar da danyen mai ne wajen shigowa da galibin tataccen man da take amfani da shi.

Masana sun yi amanna cewa akwai kumbiya-kumbiya a tsarin shigo da tataccen mai da dangoginsa, da biyan kudin shigowa da shi da ma rarraba shi.

A ganinsu, daya daga cikin hanyoyin magance wannan matsala ita ce toshe kofofin sulalewar kudaden gwamnati da tabbatar da cewa matatun man Najeriya na aiki yadda ya kamata.