✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (1)

Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga…

Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko.

Tambaya:

Assalamu Alaikum Duniyar Ma’aurata. Tambaya ta ita ce, shin an ce mace ta yi wa mijinta biyayya, duk abin da ya sa ta ta yi kuma duk abin da ya hane ta dole ta bari ko tana so ko ba ta so in dai bai ci karo da iyakokin Ubangiji ba. Shin akwai iyaka game da ladabin da za ta yi masa ko kuwa jumilla ne komai sai ta yi masa ladabi ko da ita tana matukar cutuwa a cikinsa? Shin in shi bai sauke hakkokinsa a kanta kamar ta fannin ciyarwa, tufatarwa, ilimantarwa da kula da lafiya, dole ita sai ta sauke hakkokinsa a kan ta na ladabi da biyayya da sauran su? Da fatan za ku ba ni amsar wannan tambaya don mata da yawa suna cutuwa da sunan ladabin aure.

-Hajiya Zainab daga Abuja. 

Amsa:

Lallai yana daga cikin hakkokin mata a kan mijinta yin ladabi da biyayya a kan dukkan abin da bai ci karo da dokokin Allah ba. Ana son mace ta kasance kamar baiwa ko ‘yar aiki wajen ladabi da biyayya ga mijinta. Kuma yadda Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya tsara a shari’ar Musulunci yin hakan zai zo mata da matukar sauki saboda an wajabta wa mijinta ya kula da ita, ya rika ji da ita, ko tallafa da tarairaya da kyautata mata ta kowane fanni na zamantakewa da ita. In mijinta ya sauke wannan wajabcin da aka dora masa to yin ladabi da biyayya da zama kamar baiwa zai zo wa matar da matukar sauki ba za ta ji wuyarsu ba, ko ta ji kamar bauta take yi ko ta ji ba a bakin komai take ba.

Ba inda aka yarda miji ya rika galllaza ma matarsa ko ya tsaurara mata ko ya  huldance ta kamar ita baiwa ce marar daraja ko ita ‘yar aiki ce wacce ba ta a bakin komai.

In namiji bai sauke hakkokinsa na ciyarwa, tufatarwa, ilimantarwa, kula da lafiya da kuma kyautata hulda da zamantakewa ba, duk da haka matar ta ci gaba da yi masa ladabi da biyayya da kuma kyautatawa domin don Allah take yi ba don miji ba, kuma shi ladabi da biyayya ga miji asalinsa Allah ake yi wa don Shi Ya yi umarni da hakan ba mijin ba. Amma fa sai ta yi hakan iya karfinta, kar ta yarda garin haka ta cutar da kanta ko lafiyar ta, ko ta saka kanta cikin halin kaka- ni- ka- yi ko ma ta rasa imaninta ta fara shiga bokaye da ‘yan tsibbu don neman mafita. Shi ya sa shari’a ta ba mace damar ta nemi saki in auren bai mata ba, ko in tana cutuwa a ciki ko in ma mijin yana sauke hakkokinsa amma ta ji bai yi mata ba, ba ta son sa a zuciyarta shari’a ta ba ta dama ta nemi saki kamar yadda muka gani hakan ta faru cikin Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam kuma Manzon Allah bai nuna kyamar abin ba sai dai ya goya masu baya a kan su nemi ‘yanci na fita daga auren. Shi aure an yi shi ne don a yi zaman jin dadi da kyautata wa juna, in ya kasance akwai cutarwa ga daya ko duka, neman sulhu shi ne matakin farko sannan hakuri na maganin dukkan matsala, addu’a kuma tana canja kaddara. In kuma an kasa yin hakuri to halal ne a nemi saki don kowa ya samu sa’ida.

Tambaya:

Shin ko ya halatta miji ya rika yin waya da budurwarsa a gaban matarsa har yana kyalkyata dariya? Haka mijina yake min kuma na gaya masa ba na so amma ya ki dainawa ya ce wai shi bai iya yin boye- boye ba.

Amsa:

In dai ana maganar halacci a shari’ance to ko ba a gaban matarsa ba, bai halatta garesa yin hira a kebance da budurwarsa ba, kuma haramcin ya kara tsauri har in yi kasance budurwar shan bati da bata lokaci ne ba wai auren ta zai yi ba. Yin hira da budurwa, zuwa zance, ba da kudin zance, yi wa budurwar hidimomi, daukar ta zuwa yawo da, kawo ta don gaida ‘yanuwa ko kai ta gidan uwargida duk al’ adu ne da suka ci karo da shari’a. Don haka wanda ya damu da abin da za a rubuta masa a littattafan hisabinsa sai ya nemi ilimi kuma ya guje wa wannan kazamar dabi’a.

Sannan ko da ya halatta ma yin hira da budurwa to haramun ne ka yi a gaban matarka don wannan cin fuskarta ne da neman saka ta cikin kunci da motsar mata da zafin kishi. Kuma in ta yi wani abu a dalilin haka sai a koma ana zaginta.

Haka nan ta fannin neman aure, boyewa shi ne mafi alheri har sai ya tabbata sannan a bayyanar, ko bai iya boye- boye ba to ta fannin neman ya fi masa alfanu in ya boye din.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.