Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (11) | Aminiya

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (11)

    Nabeela Ibrahim Khaleel

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko:

Tambaya:  An yi min auren dole, ina ta zaman hakuri da shi ina yi wa iyaye biyayya, ’ya’yanmu shida a halin yanzu ya tattago karin aure kuma zai auri wadda yake so ni kuma an riga an tauye min hakkina. Ni ba karatu ba, ni ba sana’a ba, saboda duk ya hana ni, kuma yanzu ya juya min baya saboda zai kara aure. Mahaifina ya rasu, na ce yayyena su raba auren amma sun ki. Ba ma zaman lafiya, ki taimaka mini da shawara.

Amsa: To auren dole dai bai halatta ba a shari’ar Musulunci kuma ko kafin a daura ko bayan an daura mace tana da ikon ta bijire wa wannan aure kuma ba ta da wani laifi don ta aikata haka. Iyaye, ko waliyyin mace bai da damar da zai tilasta ta auri wanda ba ta so. Kamar yadda ba zai tilasta a kan ta ci wani launin abincin da ba ta so ba, ko ta saya ko sanya wata tufar da ba ta so ba, to bai kamata a tilasta mata zama da mijin da ba ta so ko take kin jininsa ba. Sannan bayan daurin aure in ta ki amincewa to aure ya tashi sai ta je ga alkali ya warware wannan dauri, in kuma ta aminta ta yi hakuri to shi ke nan aure ya tabbata. Sannan ba daidai ba ne ga namiji ya rika amfani da karfi yana kwanciya da matar da aka yi wa auren dole, abin yi shi ne ya yi hakuri ya yi ta lallashi har sai ta amince da shi ko ya sake ta ya je ya nemi wata macen mai sonsa. Allah Yana son tausayi da jinkai ya tabbata a cikin rayuwar aure, to ya za a yi hakan ya samu in an tilasta wa mace auren wanda ba ta so kuma ba ta kauna.

Sannan yayyenki ba su ne za su raba aure ba, kotun Musulunci za ki kai don a raba. Wannan ya zama khul’i ke nan, za ki biya shi sadaki da wasu kyaututtuka da ya bayar a lokacin auren sai alkali ya sa shi ya ba ki sakin ko shi alkalin ya ba ki sakin.

Shawarar Duniyar Ma’aurata gare ki yake baiwar Allah! Ita ce da farko ki nemi taimakon Allah Madaukakin Sarki, kuma ki yawaita yin hakan, ki yawaita yin Sallar Istikhara, Sallar neman taimakon Allah, ki yawaita yin sadaka da Sallar tsakar dare da nufin Allah Ya dafa miki ya taimake ki ta kowane fanni a kan wannan jarrabawa da kike fuskanta.

Shawara ta biyu ita ce ki binciki kanki bincike mai zurfi: Anya kina son mutuwar wannan aure naki? Anya kina son ’ya’yanki su girma iyayensu ba a tare da juna ba? Anya  ba batun karin auren ne ya canja miki ra’ ayi ba? Anya da a ce babu maganar karin auren za ki nemi a raba auren? Shin akwai wani abu da mijinki zai miki ya sa ki hakura ku ci gaba da zama lafiya? Anya kuwa ba kishi kumallon mata ba ne yake tuko miki?

Ya kamata ki yi wa kanki wannan bincike kuma ki samarwa kanki amsoshin wadannan tambayoyi. Domin ’yar uwa auren wanda kake so ba shi ne tabbas ba, auren wanda ke mutunta ki da ba ki dukkan hakkokinki shi ne abin so, abin fata. Da yawa sun auri wanda suke so da kauna amma  bayan auren su nemi kaunar su rasa, su wayi gari sun zama makiyan juna. Kuma da yawa akwai wadanda suka yi auren so da kauna amma suna nan suna zaman hakuri, zaman ’ya’ya kamar yadda kike yi, to ina bambanci a nan?

In kin tabbatar ba ki son mutuwar aurenki kuma ba ki son ’ya’yan su girma uwa ko ubansu a gida, to sai ki bi mataki na gaba wato  ki zabi wakili daga bangarenki shi ma maigidanki ya zabi nasa wakilin a zauna a yi muku sulhu, sai ki fadi dukkan abubuwan da yake miki na ba daidai ba su kuma wakilan sulhu za su umarce shi ya gyara kuma dole  ya bi umarninsu.

In kuma kin tabbatar ke ba ki son ci gaba da zama da mijinki saboda ba ki samun natsuwar zuciya, to kina da dama ki nemi khul’i ki yi idda ki auri wanda kike so, amma da za ki yi hakuri saboda ’ya’ya da ya fi. Amma kuma in kin tabbatar kina cutuwa ainun a cikin wannan aure to ba laifi ki nemi khul’i ki fita, ’ya’ya kuma duk inda suke Allah ne Mai kula da su kuma Mai zartar da al’ amuransu.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.