Daily Trust Aminiya - Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (4)
Subscribe

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (4)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa, amin.

Tambaya: Matata ta kasance mai yawan fushi, tana da zuciya sosai nakan yi iya bakin kokarina wajen rarrashinta amma wani lokaci sai dai in kyale ta sannan in muka samu sabani ba ta san ta ba ni hakuri ba kuma ko da na kaurace mata wajen kwanciya hakan ba zai sa ta fahimci ta yi mini laifi ba, balle ta ba ni hakuri sai dai in ni na gaji da hakan na yi mata magana sai ta ce ai ita ba ta san ta yi mini komai ba. Gaskiya hakan na ci mini tuwo a kwarya sosai, a ba ni shawara don Allah.

Amsa: A Aya ta 34 cikin Suratul Nisa’i, Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana daki-daki yadda za a horar da matar da ta doge a kan yawan saba wa maigidanta, ta hanyar kin bin urmaninsa da rashin girmama shi da nuna rainin wayo ko yawan wulakanci:

“… kuma wadanda kuke tsoron bijirewarsu to ku yi musu gargadi, kuma ku kaurace musu a cikin wuraren kwanciya, sannan ku doke su. Sannan idan sun yi muku da’a kada ku nemi wata hanya a kansu. Lallai ne Allah Ya kasance Madaukaki Mai girma.”

Hanyar horarwa ta farko za a fara da nasiha mai taushi, kuma kowace mace sai a dubi yanayin halayyarta a yi mata nasiha ta hanyar da ake ganin za ta shige ta har hakan ya sa ta fahimta ta gane kurenta ta daina aikata abubuwan muzantawa ko wulakanta mai gidanta. Dole sai maigida ya yi kyakkyawan tunani da nazari da zabar kyawawan kalmomi da yake ganin za su yi saurin fahimtar da ita kurenta, sannan kuma ya sanya hakuri da sakin fuska yayin da yake gabatar da nasiha, in ma da hali ya fara da yaba mata game da kyawawan halayenta da abubuwan da suke burge shi game da ita, yadda zai sa ta ji dadi a zuciyarta. Daga nan sai ya gabatar da  abin da take yi wanda ke bata masa rai, kada ya ji kunya ko girman ka bayyana mata irin yadda dabi’ar ke tsananin bata maka rai da kuma hargitsa maka tunani, sannan ka gabatar da hadisan da suka yi bayani game da girma da matsayin miji gare ta.

Duk a cikin bayaninka ka lura kada kalaman kullata su fito kuma, kuma kada kuma ka raba bayaninka gida biyu, wani bangaren yana rarrashi wani bangaren kuma yana mai tuhumarta da ta yi kaza ta yi kaza da nuna jin haushinka a fili. Lallai ka yi dukan kokarinka kada tuhuma da jin haushi su bayyana cikin kalamanka. wannan zai sa, ko yaya ta so ta yi aiki da nasiharka, hakan zai mata wuya musamman in ba da gangan take yin abubuwan rainin ba, musamman in wannan dabi’a ta kasance daga cikin asalin dabi’unta ba wai yanayi ya kawo haka ba.

In maigida ya yi nasiha akalla sau 3, ko sama da haka in ya kasance mai tsananin hakuri, in har uwargida ta yi kunnen uwar shegu da nasihar tasa, ta ci gaba da zuba masa ruwan rainin wayo da rashin girmamawa, a nan sai ya fara yi mata gargadi kakkausa, in ya maimata haka sau uku ko adadin abin da zai iya, ba ta daina ba sai ya kaurace mata wurin kwanciya.   A lura da kyau wajen kwanciya kadai ake kaurace wa mace ban da wajen sauran al’amuran yau da kullum; amma ba laifi in aka rage sakin fuska gare ta don isar mata da cewa ta wuce gona-da-iri.

In kauracewar ba ta yi aiki ba sai duka kamar yadda ayar ta yi bayani. Amma malamai sun yi bayani cewa duka mai sauki ake yi ba mai zafi wanda zai iya raunata ta ba, kuma kada a yi shi a fuskarta, kuma kada a yi da yawa sassaukan duka wanda zai isar da sakon cewa lallai ta yi laifi sosai. Bayan nan in ta shiryu sai a ci gaba da zama da ita da alheri da kyautatawa. In kuma duk wannan bai sa ta natsu ba sai a je ga hanya ta gaba kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya yi bayani a aya ta gaba:

“Kuma idan kun ji toron sabawa tsakaninsu, to ku aika wani mai sulhu daga mutanensa da wani mai sulhu daga mutanenta; idan sun yi nufin gyarawa Allah Zai daidaita tsakaninsu. Lallai ne Allah Ya kasance Masani Mai jarrabawa.”

Ke nan sai maigida ya nemi a zauna a yi musu zaman sulhu, shi zai bayar da wakilai biyu daga bangarensa, ita ma haka, wakilan za su yi bincike ciki da waje game da matsalar, sannan su tattauna a tsakaninsu, abin da suka yanke shi ne hukuncin da za a zartar  a kan ma’aurata. In suka yi umarni ga uwargida dole ta yi kaza ko ta daina kaza to dole ta yi aiki da hukuncinsu, yin hakan shi ya yi daidai da shari’a.

Haka nan maigida kuma yana daurewa ya ci gaba da zama da ita haka nan, ya kawar da kansa  daga aibinta, ya rika yawan tuna alheranta, sannan, ya rika saurin yin yafiya gare ta a duk lokacin da ta saba masa, wannan zai saukaka wa danganta tsakaninsu kuma kila hakurinsa da kai zuciya nesa game da halayen muzancinta ya sa ta sassauto.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.

More Stories