✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tambuwal ya aza harsashin masana’antar takin zamani a Sakkwato

Masana'antar za ta rika samar da metric tonne 200,000 na takin zamani

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya kafa harsashin gina masana’antar takin zamani ta Dala miliyan 13 a Jihar.

Kamfanin OCP Africa Fertilizers Nigeria Limited na kasar Moroko ne zai yi masana’antar a rukunin masana’antu na Kalambaina, Karamar Hukumar Wamakko,  ta Jihar Sakkwato domin samar da Metric Tonne 200,000 na takin zamani a duk shekara.

“Wannan na daga cikin manufofin gwamnatin na kawo sahihan masu zuaba jari daga kasashen ketare zuwa jihar”, inji Gwamna Tambuwal a lokacin taron.

Tambuwal ya ba wa kamfanin tabbacin samun riba tare ta hanyar samun ciniki da kuma ayyuka daga gwamantin Jihar Sakkwato da zarar an kammala aikin kuma kamfanin ya fara aiki a watan Yuli mai zuwa.

Tambuwal ya kwadaitar da masu zuba jari da su je jiharsa saboda tana da wadatattun ababen da suke bukata a rukunin masana’antunta, saukin samun filaye, sassaucin haraji da kuma hadakar zuba jari.

“A wannan bangare, OCP Africa ta fara cin gajiyar tagomashin gwamnatin jihar da ta ba ta fili hekta 10 da takardar mallakarsa cikin kasa da sa’a 24.

“Gwamantinmu ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta da kara kawo cigaba ga Jihar Sakkwato a kowane bangare”, inji gwamnan.

Ya kada da cewa gwamantinsa za ta ci gaba da tallatawa da kuma bunkasa harkar noma domin samar da wadataccen abinci.

Da yake jawabi, Mataimakin Manajan Daraktan kamfanin, Caleb Usoh ya ce masana’antar za ta samar da ayyukna yi tare da zama cibiyar horo ga masu masana’antun takin zamani, manoma da sarkon masu harkar kasuwancin noma.