✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tambuwal ya kawo wa Atiku rumfar zabensa

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya kawo akwatin mazabarsa ta Sakandaren ’Yan Mata da ke Tambuwal a zaben Shugaban kasa, da Majalisar Tarayya. Tambuwal…

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya kawo akwatin mazabarsa ta Sakandaren ’Yan Mata da ke Tambuwal a zaben Shugaban kasa, da Majalisar Tarayya.

Tambuwal wanda shi ne Babban Daraktan Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku-Okowa ’yan takarar shugaban kasa da mataimaki a PDP, yana takarar Sanatan Sakkwato ta Kudu ne, kuma ya yi nasara a rumfarsa da kuri’a 252.

A zaben shugaban kasa, Atiku na PDP ya yi nasara da kuri’a 250, yayin da Tinubu na APC ya samu kuri’a 44.

Kazalika a bangaren kujerar majalisar wakilai, PDP ta yi nasara sa kuri’a 247 yayin da APC ta samu 45.

Idan za a iy tunawa, Tambuwal yanje daga neman takarar shugaban kasa a PDP ya mara wa Atiku baya, wanda a karshe ya yi nasara a zaben fid-da gwani.