✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarihi da rayuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris (1937-2020)

Muhimman abubuwa da ya kamata ku sani a kan Sarkin Zazzau

A ranar Lahadi 20 ga Satumba, 2020, Allah Ya yi wa Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, bayan shekara 45 a kan karagar mulki.

Alhaji Shehu Idris ya rasu ne a Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna bayan fama da ranshin lafiya, kuma a ranar aka binne shi.

Aminiya ta tattaro muku muhimman abubuwa da za ku so ku sani game da rayuwar margayi Sarki Shehu Idris, daya daga cikin manyan sarakunan Arewancin Najeriya.

Mai martaba sarki mutum ne masani, sannan kuma abin girmamawa a duk fadin Arewa da sauran sassan Najeriya.

Daga cikin hikimomi da Allah Ya yi masa ita ce tafiya da mutane a cikin mulkinsa, yakan tuntubi jama’a a kan abubuwan da ka-je-su-zo.

  • Haihuwarsa

An haifi Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dokta) Shehu Idris a 1937.

Shi dan Malam Idris autan Sambo ne dan Sarkin Zazzau na 10. Malam Muhammadu Sambo kuma da ne na Sarkin Zazzau na uku Malam Abdulkarimu Bakatsine.

  • Karatunsa

Shehu Idris ya fara karatunsa na addini ne tun yana dan shekara biyar a hannun Malam Bawa da kuma Malam Abubakar da ke Unguwar Iya a garin Zariya.

A 1947, lokacin yana da shekara 11, ya fara karatun zamani a makarantar Elemantare ta Zariya (Zaria Elementary School).

Daga nan sai Makarantar Midil ta Zariya daga 1950 zuwa 1955.

Bayan ya kammala sai ya wuce zuwa Kwalejin Horar da Malamai ta Katsina (KTC) inda ya kammala a 1958.

  • Gogewa a aiki

Bayan kammala karatunsa a Katsina, Alhaji Shehu Idris ya fara karantarwa a makarantar firamare ta garin Hunkuyi —Jihar Kaduna— a 1958.

Daga Hunkuyi sai aka mayar da shi garin Zangon Aya, sannan Paki duk a matsayin Shugaban Makaranta (Hidimasta).

Daga Paki sai aka mayar da shi Zariya a matsayin Hedimastan Makarantar Firamare ta Kaura.

A 1960 ne ya Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya ba shi mukamin Babban sarakatare na musamman na sarki.

Daga nan ne sai aka nada shi sarauta, ya zama wakilin ofis, wato mai daukar nauyin duk abin da ya shafi aikin masarauta a karkashin ‘Native Authority’ a Zariya a 1963.

A shekarar ce aka nada shi Danmadamin Zazzau, Hakimin Birni da Kewaye a 1963, sarautar da ya rike har zuwa zamowarsa Sarkin Zazzau.

  • Zamowarsa Sarki

Bayan rasuwar Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu,  a 1975, sai masu zaben Sarkin Zazzau suka zabi Alhaji Shehu Idris a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

Zaben nasa ya samu amincewar Gwamnatin Jihar Arewa ta Tsakiya wacce ke da hedikwata a Kaduna, a zamanin mulkin Gwamnan Soja Manjo Abba Kyari.

Hakan ce ta mayar da Alhaji Shehu Idris Sarkin Zazzau na 18 a jerin Sarakunan Fulani, sannan Sarki na 3 a zuriyar Katsinawa.

  • Lambobin yabo da girmamawa

Sarki Shehu Idris ya dade yana bayar da gudunmawa, musamman ta fuskar zaman lafiya da hadin kai.

Hakan ta sa Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya samu lambobin yabo da girmamawa da dama a ciki da wajen Najeriya.

Lambobin sun hada da Digirin Girmamawa na Dokta daga Jami’ar Kimiyya ta Tarayya, Minna; da Jami’ar Najeriya, Nsukka da Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya da kuma Jami’ar Abuja.

A shekarar 2006, Kungiyar Tsofaffin Dalibai ta Jami’ar Ahmadu Bello, ta karrama shi da lambar girmamawa kan gudunmawarsa  ga cigaban kasa.

Mun ciro wannan tarihi na Mai martaba Sarkin Zazzau ne daga littafin: Dalhatu U. (2002). Malam Ja’afaru ɗan Isyaku, The Great Emir of Zazzau, wallafar Woodpecker Communication Limited. Zariya, Najeriya.