Tarnaki a Faransa bayan Bayern Munich ta lallasa PSG | Aminiya

Tarnaki a Faransa bayan Bayern Munich ta lallasa PSG

Hoto: Getty images.
Hoto: Getty images.
    Ishaq Isma'il

Rikici ya barke bayan tashi daga wasan karshe na gasar Zakarun Turai tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da Paris Saint-Germain inda Bayern ta yi wa PSG 1-0.

Kafofin sadarwa da dama sun ruwaito cewa, fusatattun magoya bayan PSG a birnin Paris na kasar Faransa sun tayar da tarzoma inda suka rika kone-konen motoci da fashe gilasai na tagogin shaguna saboda rashin nasara da kungiyar da suke goyon baya ta yi.

Dubban magoya ne dai suka taru a farfajiyar filin wasa na Parc des Princes da kuma babban titin Elysees domin mara wa kungiyar PSG baya yayin kallon wasan a babban allo.

Tarihi ne ya maimaita kansa yayin da ta Bayern Munich ta sake lashe gasar ta Zakarun Turai bayan ta lallasa Paris Saint-Germain da ci daya mai ban haushi.

Takaicin wannan lamari ya sanya magoya bayan PSG suka tayar da rikici har ta kai su ga yin arangama da ’yan sanda daura da filin wasan na Parc des Princes.

Rundunar ’yan sandan Faransa cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin kan shafinta na Twitter, ta ce ta cafke akalla mutum 148 wadanda suka hau dokin zuciya ta tayar da zaune tsauye.