✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron APC: Hadin kai ko dinkin gangar auzunawa?

Shin za a dinke barakar da ta kunne kai a jajibirin babban taron APC?

A ranar Asabar Jam’iyyar APC mai mulki za ta gudanar da babban taronta na kasa, wanda aka jima ana dagewa saboda dalilai iri-iri.

A babban taron ne jam’iyyar za ta zabi sabbin shugabanninta na kasa, wadanda za su ci gaba da jan ragamarta a matakin kasa da kuma shiyyoyin siyasa shida na Najeriya.

Taron da kuma abin da zai haifar shi ne zai nuna hakikanin halin da APC ke ciki na hadin kai ko barakar da ake zargin ta kunno kai kan zaben shugabannin jam’iyyar, wanda ake zargin ya nemi sawa a yi baram-baram tsakanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin jam’iyyar.

Rabon APC da samun zababben shugabanci a mataskin kasa, tun bayan da kotu ta soke Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Kasa wanda tsohon Shugaban Jam’iyyar, Adams Oshiomhole, ya jagoranta.

Bayan korar Oshiomhole da kotu ta yi bayan wasu mambobin jam’iyyar sun maka shugabancinsa a kotu, APC ta nada tsohon sakatarenta na kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe a yanzu, Mai Mala Buni, a watan Yunin 2020, ya zama shugaban riko, sulhu da kuma tsara babban taron.

Amma gudanar ta taron, wanda a nan za a zabi shugabannin jam’iyyar ya yi ta fama da mataloli iri-iri.

Matsalolin sun hada da karar da wasu ’ya’yan jam’iyyar suka kai kotu suna kalubalantar halascin shugabancin Buni, kafin daga karshe dai kotu ta yi watsi da karar ta kuma amince a yi taron da zai wakana ranar Asabar 26 ga Maris, 2022.

An shirya  wa taron

Tuni aka kawata dandalin Eagles Square da ke Abuja, inda za a gudanar da taron, wanda a wurin deliget 7,000 za su jefa kuri’ar zaben sabbin mutanen da za su ja ragamar APC a matakin kasa da shiyyoyin siyasa.

Rundunar ’Yan Sanda ta Birnin Tarayya, Abuja, ta sanar cewa ta girke jami’anta akalla 1,815 domin samar da tsaro da bin doka da oda a wurin taron.

’Yan kasauwa kuma tun ranar Alhamis suka yi wa wurin tsinke da hajojojinsu na abinci da sauran kayayyaki, suna masu fatan samun riba mai tsoka.

Bincike ya gano cewa otal-0tal da ke Abuja sun cika makil da kwastomomi, a sakamakon bakin da ke tuturuwa daga sassan Najeriya zuwa birnin domin halartar taron na APC.

Ma’aunin hadin kan Buhari da gwamnoni

Taron na zuwa ne jim kadan bayan dambarwar shugabancin da ta dabaibaye jam’iyyar, kan shugabancinta na riko da kuma shugabancinta mai shigowa.

Makonni kadan kafin ranar taron ne aka shiga rudani game da matsayin Buni a jam’iyyar, inda kwatsam Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya wayi gari a matsayin Mukaddashin Shugaban Riko bayan Buni ya tafi duba lafiyarsa a kasar waje.

Gwamna Abubakar Bello ya ce Buni ya mika masa ragamar jam’iyyar, amma da aka yi mishi tambaya game da gaskiyar labarin tsige Buni, sai ya ce shi bai san makomar Buni ba.

Ana cikin haka Gawmnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce Buhari ne ya ce su tsige Buni saboda zargin shi da yi wa jam’iyyar zagon kasa, matakin da Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, ya tabbatar ya kuma yaba da kokar Bunin.

Ana cikin haka shugabancin Bello ya sanar da dakatar da Sakataren Rikon APC, Sanata John James Akpandeodehe, wanda shi ne ya saba gudanar da jam’iyyar idan Buni ba ya nan, ya kuma kalubalanci shugabancin na Bello.

Tufka da warwara

An kuma tambayi Gwamna Bello game da wata takarda da aka gani cewa Buni ya ba shi rikon jam’iyyar amma ya ce bai san da takardar ba.

Hakan kuwa ya zo ne bayan an ga bullar Buni a London tare da Buhari, wanda ya je ganin likita, inda Buharin ya bukaci jam’iyyar ta kyale Buni ya ci gaba da aikinsa, har a yi babban taro.

Wannan ya sanya alamar tambaya game da gaskiyar abin da ya faru, shin Buhari ya yi amai ya lashe ne, ko kuma kage aka yi mishi kan tsige Buni?

Da jin haka ne Sanata Akpandeodehe ya ci gaba da aiki, har ya jagoranci kaddamar da sayar da takardun neman takarar shugabancin jam’iyyar ga masu bukata.

Daga baya sai ga Buni ya bulla yana cewa yana tabbatar da shugabancin rikon Bello wanda ya ce ya mika wa ragamar gudanar da jam’iyyar da shirye-shiryen taron a rubuce, har ya bukaci a ba shugabancin Bello hadin kai.

Wasikar ta Buni ta kuma tabbatar da halascin Bello da duk hukuncin da shugabancin ya yanke, har sai ya dawo.

Bayan nan ne dai wata takarda ta fito dauke da sa hannun kwamitin rikon jam’iyyar cewa ta riga ta sallami Sakataren Rikon Jam’iyyar, tun a ranar 28 ga watan Fabrairu.

Amma kuma bayan dawowar Buni, wanda Bello da sauran kusoshin jam’iyyar suka je suka yi mishi barka da zuwa, sai aka gan shi tare da Sanata Akpandeodehe a hedikwatar jam’iyyar sun ci gaba da aiki.

Tana kasa tana dabo

Wasu dai na zargin akwai wata kullalliya da ba ta riga ta bayyana ba tukuna, musamman ganin cewa wasu kusoshin jam’iyyar da suke son yin takarar shugaban kasa a jam’iyyar na kokarin ganin yadda masu goyon bayansu za su samu madafun ikon jam’iyyar.

Uban Jam’iyyar na Kasa, Bola Tinubu, da Mataimakin Shugaban Kasa, wanda ake ganin yaronsa ne, duk suna neman takarar shugaban kasa.

A bangare guda kuma ana zargin gwamnoni na son wani daga jikinsu ya samu wannan dama domin su mara mishi baya.

Zabin Buhari

A jajibirin babban taron na APC, babbar matsalar da ta kunno kai ita ta takarar shugabancin jam’iyyar.

Buhari, a cewar rahotanni, ya zabi tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, a matsayin dan gaban goshinsa da za a ba wa kujerar shugaban jam’iyyar tare da wasu mutum biyar da za a nada a Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Kasa, ba tare da hamayya ba, amma gwamnoni suka yi mishi ca.

A kan haka ne Buharin ya yi zama da su domin samun amincewarsu da Abdullahi Adamu da sauran mutum biyar din da yake so a ba wa mukamai a kwamitin gudanarwar jam’iyyar.

Rabuwar kan gwamnoni

Bayan fito gwamnonin jam’iyyar 16 da mataimakan gwamnoni biyu daga zaman, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Gwamna Atiku Bagugu na Jihar Kebbi, ya sanar da abin da ya faru, ya kuma ce sun nuna wa Buhari amincewarsu da mutum biyar din.

Bagudu ya ce bayan sun yi wa Buhari bayanin kokarin da suke yi a kowane yanki domin samun nasarar babban taron, sai ya ba su wa’adin awa 24 su je su tattauna su fitar da jerin sunayen ’yan takarar da za a ba wa shugabancin babu hamayya domin samun lumana da hadin kan jam’iyyar.

Ya ce a lokacin zaman, Buhari ya ba da umarnin a biya sauran ’yan takarar kujerar kudaden da suka kashe na sayen takardar neman takara.

Bayan nan ne Buhari ya yi zama da sauran ’yan takarar da suka yanki takardar takara tare da Sanata Abdullahi Adamu, yana neman su goyi bayan Abdullahi Adamu.

Rahoton da muka samu ya nuna ’yan takarar sun nuna amincewarsu, tare da yi wa Abdullahi Adamu fatan alheri, har suna cewa sun so a ce an yi zaman da su tun kafin nan.

Amma daga baya sai ga rahoto wasu daga cikinsu na cewa ba su janye takararsu ba.

Kazalika, kasa da awa 24 bayan zaman Buhari da gwamnonin, aka samu rabuwar kai a tsakanin gwamnonin, inda Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti ya ce bai sai da batun ba.

Wasu gwamnonin kuma sun ta tabbatar cewa Buhari ya zabi Abdullahi Adamu kuma ya bukaci su mara mishi baya.

A yayin da ake hakan kuma, Buhari ya yi zama da iyayen jam’iyyar da manyan kusoshinta a Majalisar Tarayya domin, inda ya yaba musu kan goyon baya da fahimtar da suka nuna wa gwamnatinsa, yana kuma neman hadin kansu wajen ganin an gudanar da taron cikin lumana.

Bisa duka wadannan abubuwa, shin ana iya cewa APC ta dinke baraka, ko kuma dinkin gangar auzunawa aka yi?

Wasu majiyoyi na cewa sai a ranar taron wadansu masu neman takara za su janye, karshenta tabbatarwa da sunayen da ke cikin ‘Unity List’ kawai za a yi a taron.

Amma akwai masu ganin yiwuwar kallo zai koma sama a wurin taron — wadanda aka yi wa ba daidai ba, ko ba su gamsu ba, suna iya tattara nasu su fice daga jam’iyyar ko ma su yi a-yaga.

Ko ma mene ne, sakamakon taron na ranar Asabar shi ne zai rabe aya da tsakuwa.