✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron Tattaunawar Daily Trust karo na 20 na gudana

Taken taron shi ne: Bibiyar Manufofin ’Yan Takarar Shugaban Kasa a 2023.

A wannan Alhamis din, 26 ga Janairu, 2023 Taron Tattaunawar Daily Trust karo na 20 yake gudana a Abuja, babban birnin Najeriya.

Taron mai taken: Bibiyar Manufofin ’Yan Takarar Shugaban Kasa a 2023 na gudana ne kai tsaye a Dakin Taro na Cibiyar Sojin Sama da ke Abuja, wato NAF Center.

A kwana da sanin cewa, Kamfanin Media Trust Limited mai wallafa jaridar Daily Trust, Aminiya da Gidan Talabijin na Trust da kuma Trust Rediyo ne ya dauki nauyin wannan tattaunawar kamar yadda ya saba.

A yau din ne wasu fitattun ‘yan Najeriya hudu za su nazarci alkawurran yakin neman zaben na ’yan takarar Shugaban Kasa a Zaben 2023 yayin taron tattaunawar.

A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Kamfanin na Media Trust Limited, Mounir Gwarzo ya fitar, ya ce tattaunawar za ta kai ga masana su samar da mafita da kuma isar da abin da suke ganin ya kamata Shugaban Najeriya na gobe ya mayar da hankali a kai don kawo sauyi ga kasar nan.

Malam Gwarzo ya ce an zabi mutum hudu wadanda za su yi sharhi gami da musayar ra’ayi kan manufofin masu takarar shugabancin Najeriya a zaben da ke tafe.

Wadanda za su yi sharhin a yayin taron sun hada da Mista Jibrin Ibrahim na Cibiyar Dimokuradiyya da Ci Gaba (CDD); sai fitacciyar ‘yar kasuwa kuma tsohuwar Shugabar Hukumar Gudanarwa ta Bankin First Bank (FBN), Misis Ibukunoluwa Awosika.

Haka kuma, akwai kwararre a fannin bunkasa dan adam, Dokta Eugene Enahoro da kuma malami a fannin nazarin matsalolin kasuwanci a Makarantar Kasuwancin Legas, Dokta Yetunde Anibaba.

Babban Limami kuma Shugaban Majalisar Limamai na Cocin Katolika da ke Abuja, John Cardinal Onaiyekan, ne zai jagoranci taron shekara-shekara karo na 20, wanda Mataimakin Babban Edita kuma Shugaban Kwamitin Editoci na Jaridar Daily Trust, Dakta Suleiman Suleiman zai jagoranta.

Gogaggen dan jarida kuma Sarkin Karshi da ke Abuja, Alhaji Ismaila Mohammed, MFR, zai kasance Uban Taro.

Sabanin yadda taron ya gudana daga nesa shekaru biyu da suka gabata, wannan karon zai sami haduwa ta kiri da muzu bayan cire takunkumin da aka sanya saboda annobar COVID-19.

Ga masu son bibiyar tattaunawar, taron na bana za a watsa shi kai tsaye ta gidan talabijin na Trust a tashar StarTimes Channel 164; Talabijin ta NigComSat’s Free TV; Moreplex 715; ArabSat Badar Sat7; AVO TV; da LIMEX World TV, da kuma shafin YouTube da sauran dandalai na kafofin watsa labarai.