✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron Tinubu: An tsaurara tsaro a Gidan Gwamantin Kano

An tsaurara matakan tsaro a Gidan Gwamnatin Jihar Kano, inda ake ta taron zagayowar ranar haihuwar Jagoran Jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu. Tun…

An tsaurara matakan tsaro a Gidan Gwamnatin Jihar Kano, inda ake ta taron zagayowar ranar haihuwar Jagoran Jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Tun dai manyan suka taru a Gidan Gwamnatin domin taron na cikar Tinubu, wanda ya ziyarci Kano, shekara 69 da haihuwa.

An kuma girke jami’an tsaro a muhimman wurare daban-daban a kwaryar birnin Kano, musamman a yawancin tituna da shataletale da mahadar tinuna a cikin garin.

Kazalika an jibge karin jami’an Hukumar KAROTA, mai kula da ababen hawa ta Jihar.

Lokacin da ake shriye-shiryen taron a Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Taron na Tinubu na zuwa ne a ranar kuma a Majalisar Sarakunan Najeriya ke gudanar da Babban Taronta karo na 12 a Kano.

Kazalika an girke kwatankwacin jami’an a Titin Magajin Rumfa, inda ake taron Majalisar Sarakunam.