✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tashin Dala: Farashin ruwan leda ya koma N20 a Kogi

Mun yi la’akari da yanayi na tattalin arziki da ake fama da shi a yanzu.

Farashin ruwan leda ya yi tashin gwauron zabo a Jihar Kogi inda aka koma sayar da duk leda guda a kan Naira 20.

Farashin ruwan leda ya tashi daga kan naira 10 zuwa 20 kamar yadda Kungiyar masu yin ruwan ledar ta bayyana.

Kungiyar da ke bayyana takaicinta a kan wannan lamari, ta yi bayanin cewa yana da alaka ne da hauhawar farashin da dala take yi a kasuwar canjin kudi ta kasar.

A bara ne kungiyar ta yi karin farashin duk jakar ledar ruwan daga Naira 100 zuwa Naira 130 saboda abin da ta kira matsin tattalin arzikin da annobar Coronvirus ta haifar.

Da yake zantawa da wakilinmu a ranar Laraba a Lakwaja, babban birnin Jihar Kogi, Mista Joseph Esseyin, shugaban kungiyar masu yin ruwan ledar ya ce a halin yanzu ana sayar da ledan ruwan a kan Naira 200 duk jaka, la’akari da yanayi na tattalin arziki da ake fama da shi a yanzu.

A cewarsa, matakin kara farashin ruwan ledar ba manufa ba ce ta ci gaba da tsananta tsadar rayuwa da al’umma suke fama da ita ba a yanzu, illa iyaka yanayin da karin farashin kayyakin sarrafawa da kuma samar da ruwan ledan ya janyo wanda a cewarsa yana da nasaba ne da ka’idodin da Hukumar NAFDAC mai Kula da Ingancin Kayayyakin Abinci da Magunguna ta shimfida.

Eseyin ya ce a yayin da farashin man fetur ya kai Naira 165 duk lita, haka kuma farashin ledar da ta kasance mazubin ruwan ya kai Naira 7000 duk tan daya.

Kazalika, Eseyin ya ce a yanzu da farashin ruwan ledar ya koma Naira 20 a Jihar Kogi da kewaye, ya bukaci dillalan ruwan ledar da su bai wa kungiyarsu hadin kai a kan lamari da ya zame mata tilas.