✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tashin Dala: Gwamnan CBN ya sauka kawai —PDP

Farashin Dala yan ninka sau uku a shubabancin Emefiele a CBN.

Jam’iyyar PDP ta bukaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya sauka daga mukaminsa saboda tashin gwauron zabon farashin Dala da kuma lalacewar tsare-tsaren kudade  a Najeriya.

Sakataren Yada Labaran PDP, Kola Olagbondiyan, ya ce shugabancin Emefiele a CBN, a karkashin gwamnatin jam’iyyar APC shi ne lokacin da tsarin kudaden Najeriya ya fi shiga mawuyacin hali har farashin Dala ya ninku fiye da sau uku.

Ologbondiyan ya ce, “Ya kamata a tuna cewa lokacin da aka nada Emefiele a matsayin Gwamnan CBN a 2014 farashin cajin Dala N164 ne.

“Amma zwau yanzu da CBN a karkashin Emefiele da gwamnain APC, farashin Dala ya kusa kaiwa N600, lamarin da ke neman durkusar da tattalin arzikin Najeriya.

“Abin takaicin shi ne shugabancin Emefiele a CBN ya gaza a babban aikinsa na gudanar da  tsare-tsaren tattalin arziki, amma yake ta yada farfaganda sabanin abin da ke faruwa a zahiri a bangaren na tattalin arziki,” inji shi.