Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK) | Aminiya

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Ya ku masu bibiya tare da aiko sakonni a wannan fili! Ina muku gaisuwa tare da jinjinar jimirin bibiya. Haka kuma ina ba ku shawarar da ku rika turo sakonninku ta WhatssApp ko tes a lambar (08020968758) ko ta I-Mel, bashir@dailytrust.com Haka kuma ku rika sanya suna da adireshi da lambar waya a kasan sakon, idan kuma ba ku son a saka lambar wayarku a jarida, sai ku sanar. Har yanzu dai muna kara tambaya, wane gida kuke, GIDAN UWARGIDA FARIDA KO GIDAN AMARYA SARATU? Allah Ya sa mu dace. A wannan makon kuma ga wasu daga cikin sakonninku, kamar yadda aka saba:

 

Daga Asiya Mukhtar Katsina:

Salam, barka da aiki FDK da kuma al’ummar wannan dandali mai albarka. Ina gaisuwa ga masoyana da kuma makiyana. Sakon gaisuwa ga masoyina Hassan Funtuwa.

 

Daga Yusif A. Adam Abdullahi (09067851381):

Salam, ina jinjina ga FDK da masu jimirin bibiyar wannan shirin a duk inda suke. Gaskiya ne, abin da kake so yakan sa mutum ya zauce. In har kana so da gaskiya, komai za ka iya fada a kansa in har bai saba wa Musulunci ba. Ina mika gaisuwata ga masoyana, Sayyada A’isha da ke Rijiyar Lemo da Isma’il Kano.

 

Baffa Maigari Gumel (07066343468):

FDK, Ina muku fatar alheri tare da dimbin masoya wannan fili. Gaskiya ni ba abin da zan ce da ku sai godiya ga wannan filin saboda ta dalilinsa ne ga shi har yanzu muna tare da masoyiyata, abar kaunata, wadda muka hadu da ita sanadiyar wannan filin a 2015. Don Allah FDK, a taimaka a shigar da gaisuwata ga ma’abota filin nan.

 

Daga Yusha’u T/Mafara:

Assalamu alaikum FDK, na farko ina son in shaida maka cewa ina tare da ku, tun da kuna tare da jaridata, wato Aminiya mai kece gaskiya. Allah kara arziki. To ni dai na hannun damar Uwargida Farida ne, mai hakuri yana tare da Allah.

 

Daga Dan Jos:

Barka FDK, wai ina masu goyon bayan Saratu? Yanzu sun daina ba ta kuri’a. Da ma a rayuwa ba a saurin yabo ko kushe sai tafiya ta yi tafiya. Allah Ya kyauta. A rika bincike kamar yadda addini ya tabbatar kafin soyayya.

 

Daga Shamsuddeen Sulaiman Ahmad (08036778553):

Salam FDK, da fatar kuna cikin koshin lafiya. Gaskiya mata ba su da alkawari, sakamakon abin da ya faru da ni da abar kaunata, har nakan kira ta da rabin jiki, da na rasa ta gara in rasa idanuna. Ba ni da wani buri da ya fi in gan ta a cikin farin ciki. Mun dauki shekara biyar muna tare. Ni ma’aikacin lafiya ne a Jihar Bauchi, a 2019 Disamba na tura gidansu domin a yi maganar aure. Da na tuntube ta sai ta ce ita fa ta fasa aure saboda ba za ta iya zama a Karamar Hukumar Takai ba, sai dai in kama gidan haya a Kano. A tunanina wannan shi ne kora da hali, ni ne ba a so ko garin?

 

Daga Shafi’u Electrician Zamfara (08025879256):

A gaskiya ina bangaren Uwargida Farida, don kuwa kowace mace tana bukatar abokiyar zama ta kwarai. Na gode FDK, Allah kara basira.

 

Daga Nafi’u Alhasan Adam Bichi (09030685335):

Fatar alheri a gare ku masu bibiyar wannan labari na Jidalin Kishiya daga jaridar Aminiya, aminiyata, aminiyar duk wani mutun nagari. A gaskiya ina bayan Uwargida Farida amma ta kara gyara halayenta, don zaman aure take ko don gudun kada mafarki ya zama gaskiya, na a yi mata kishiya. Sakon gaisuwata a gare ka FDK da Malam Nasidi Abubakar Gwauron Dutse Kano.

 

Daga Sani Dankatsina Lafiya (08034010481):

Assalamu alaikum FDK, yaya aiki? Sannu da kokari. Ni dai in bayan Uwargida baiwar Allah Farida. Allah Ya taimake ki. A karshe ina ba FDK shawara da ka rika sa mana hotuna, kamar zaman Saratu da kawarta da dai sauransu. Ina gaida masoyiyata Zahra’u Baba.

 

Daga Yunus M. Saleh (08056333326):

Assalamu alaikum FDK, fatar kana lafiya. To ke Malama Asma’u mene ne amfanin kasancewarki a gidan Saratu? Ke da kanki kika kira ta da “watsatttsiya,” kin ga kuwa ko kadan bai kamata ba. Kawai ki dawo gidan Aunty Farida (zuma farar saka), ko kina son kishiyarki ta zama mai hali irin na Saratun ne?

Ni fa labarin nan da a ce gaskiya ne, sai na yi karar Alhaji Baba. Kawai ya saki Farida ni na aure ta saboda ba kalarsa ba ce. Don irin wadannan matan suna da wahalar samu a wannan zamani. Duk da na san abokaina za su yi mini dariya, su ce na fara da bazawara amma ni hakan ba zai dame ni ba.